NNPCL: Mele Kyari Ya Aiko Sako daga Kasar Waje bayan Ba da Umarnin Kama Shi
- Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Malam Mele Kyari, ya ce ya yi mamakin sammacin kama shi da Majalisar Dattawa ta fitar
- Ya bayyana cewa tun a watan Mayu da ya gabata ya sanar da kwamitin majalisar cewa zai tafi domin duba lafiyarsa a kasashen waje
- Kyari ya ce bai samu wata sabuwar gayyata daga kwamitin ba kafin a fitar da sammacin, yana mai tabbatar da cewa zai kawo kansa idan ya dawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana sammacin kama shi da Kwamitin Majalisar Dattawa ya fitar a matsayin abin mamaki matuka.
A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin, Kyari ya ce tun da farko ya sanar da majalisar cewa yana wurin duba lafiyarsa a kasar waje, lamarin da ya hana shi halartar zaman binciken.

Source: UGC
Me ya hana Mele Kyari zuwa majalisa?
Kyari ya bayyana cewa a wasikar da ya rubuta ranar 11 ga Mayun 2026, ya sanar da kwamitin cewa yana jinya a wajen Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce a cikin wasikar, ya kuma bayyana shirinsa na amsa gayyatar kwamitin da zarar ya dawo gida Najeriya
"Na bayyana cewa a shirye nake na girmama gayyatar kwamitin da zarar na dawo Najeriya," in ji shi.
Ya kara da cewa har yanzu yana da niyyar ba da cikakken hadin kai ga binciken da ake gudanarwa.
Mele Kyari ya musanta kin amsa gayyata
Tsohon shugaban NNPCL ya musanta zargin cewa ya yi biris da gayyatar Majalisar Dattawa, inda ya ce bai ga wata sabuwar gayyata daga kwamitin ba kafin a bada sammacin kama shi.
Malam Mele Kyari ya bayyana cewa yanayin lafiyarsa a halin yanzu ne ya hana shi damar halartar zaman kwamitin kai tsaye.

Kara karanta wannan
Mele Kyari: Kwamitin majalisa ya umarci cafke tsohon shugaban NNPCL kan badakalar N210trn
Ya bukaci majalisar da ta rika tura duk wata tambaya ko bukatar bayani ta hannun lauyoyinsa har sai ya kammala jinyarsa.
Ya kare ayyukansa a kamfanin NNPCL
Da yake magana kan lokacin da ya jagoranci NNPCL, Kyari ya ce shi da tawagarsa sun sauya kamfanin daga asarar kudi zuwa samun riba.
Ya ce dukkan mu'amalolin da aka gudanar a lokacin mulkinsa, yana da cikakkun bayanai da za a iya bincika.
"Ina godiya ga kasata saboda damar da ta ba ni na yin aiki da cikakken sadaukarwa da gaskiya," in ji shi.

Source: Facebook
Majalisar Dattawa na binciken NNPCL
A kwanakin baya ne Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kudaden gwamnati ya fitar da sammacin kama Kyari bayan ya kasa halartar wani zama da aka shirya.
Kwamitin na binciken bayanan kudi da mu'amalolin NNPCL, ciki har da wasu kudade da suka haura Naira tiriliyan 210 da ake nazari a kansu, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sai dai Kyari ya jaddada cewa ba shi da abin boyewa kuma zai ci gaba da ba da hadin kai ga binciken da majalisar ke yi da zarar ya samu damar dawowa Najeriya.
NNPCL ya caccaki matatar Dangote
A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin NNPCL ya zargi matatar Dangote da kokarin mallake kasuwar mai ta Najeriya ita kadai.
Wannan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta kai kamfanin gaban kotu, tana kalubalantar yadda aka bayar da lasisin shigo da mai ga wasu ‘yan kasuwa.
NNPCL ya ce idan kotu ta amince da bukatar Dangote na soke ko takaita lasisin shigo da mai, hakan zai rage gasa a kasuwar fetur.
Asali: Legit.ng

