Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya nuna yatsa ga jam'iyyar APC bayan daba sun farmaki Ataoja na Osogbo. Ya ce an harbi basaraken ne a cikin fadarsa.
Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shirin kulla yarjejeniya da Iran domin kawo karshen yaki. Shugaba Trump ya ce za a hana Iran mallakar makamin nukiliya.
Jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta yi magana kan batun cewa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar ficewa daga cikinta.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nuna cewa an cimma yarjejeniya da Iran. 'Yan majalisar jam'iyyar Democrats sun yi masa raga-raga kan yarjejeniyar.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya soki mahukunta a Iran kan batun yarjejeniyar da za a kulla. Trump ya bayyana cewa ko kadan ba su da daraja.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan hari da ya jawo asarar rayuka a Kebbi. Gwamnatin jihar ta jajantawa mutanen da suka rasa iyalansu a harin.
Yan kasuwa sun fara lissafin miliyoyin Naira da suka tafka asarar a wata mummunar gobara da ta auku a kasuwar kayan gida ta Kingsway da ke jihar Kano.
Miliyoyin masu amfani da Facebook da Instagram sun fuskanci matsala bayan dandalin Meta ya samu tangarda da ta shafi shiga da aika sakonni a ranar Juma'a.
Mai magana da yawun bakin gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zarge-zarge kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari