Najeriya Ta Yi Maganar Mallakar Makaman Nukiliya a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Najeriya Ta Yi Maganar Mallakar Makaman Nukiliya a gaban Majalisar Dinkin Duniya

  • .Najeriya ta ce kawar da makaman nukiliya gaba ɗaya ce hanya mafi tabbas ta hana amfani da su ko barazanar amfani da su
  • Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce ƙasar ba ta mallaki makaman nukiliya kuma tsaronta bai dogara da su ba
  • Najeriya ta buƙaci ƙasashen da ke da makaman nukiliya su cika alkawurran lalata makaman da suka rataya a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin New York, Amurka - Najeriya ta yi kira da a kawar da makaman nukiliya gaba ɗaya daga doron kasa.

Najeriya ta yi gargadin cewa bai kamata bil’adama ta ci gaba da dogaro da makaman da za su iya shafe rayuwar ɗan Adam ba domin tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

Maganganun da Sarkin Musulmi ya yi wa Peter Obi da Kwankwaso a fadarsa

Najeriya na neman a kawar da makaman nukiliya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amb. Jimoh Ibrahim, ya yi wannan kiran ne ranar Talata a wani babban taron MDD kan lalata makaman nukiliya da aka gudanar a New York, cewar rahoton jaridar Vanguard.

An gudanar da taron ne domin tunawa da Ranar Ƙasa da Ƙasa ta Kawar da Makaman Nukiliya Gaba Ɗaya, a yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Kawar da makaman nukiliya ita ce hanya mafi tabbas

Jimoh ya ce Najeriya ta yi amanna cewa kawar da makaman nukiliya gaba ɗaya ita ce hanya ɗaya tilo da za ta samar da cikakkiyar kariya daga amfani da su ko kuma barazanar amfani da su.

Ya ce har yanzu akwai dubban makaman nukiliya a duniya, yayin da ƙasashen da ke mallakarsu ke ci gaba da sabunta makamansu a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar rikice-rikicen siyasar ƙasashen duniya.

Hakazalika ya kuma ce wannan yanayi na ƙara matsin lamba kan tsarin duniya na hana yaduwar makamai da kuma yarjejeniyoyin da suka shafi sarrafa makamai.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sabon rikici ya barke a Taraba, rayuka sun salwanta

“Najeriya ta yi amanna da cewa hanya ɗaya tilo da za ta samar da cikakkiyar kariya daga amfani da makaman nukiliya ko barazanar amfani da su ita ce kawar da su gaba ɗaya,” in ji shi.

Najeriya ba ta dogara da makaman nukiliya

Jakadan ya bayyana cewa Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya kuma ba ta taɓa ɗaukar shirin kera irin waɗannan makamai a matsayin wata hanya ta kare tsaron ƙasa ba, Tribune ta kawo rahoton.

“Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya, ba ta taɓa bin wani shiri na kera makaman nukiliya ba, kuma ba ta da niyyar yin hakan. Tsaronmu bai dogara da makaman nukiliya ba,” in ji Jimoh.

A cewarsa, ya kamata a gina tsaro mai ɗorewa a duniya bisa tattaunawa, dokokin ƙasa da ƙasa, haɗin gwiwar ƙasashe da kuma samar da tsaro daidai wa daida ga dukkan ƙasashe.

Jimoh Ibrahim ya yi magana a taron UNGA
Bianca Ojukwu tare da Ibrahim Jimoh a babban taron UNGA Hoto: Jimoh Ibrahim CFR, OFR
Source: Facebook

Rasha ta yi barazanar harba makamin nukiliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kasar Rasha ta bayyana cewa za ta ɗana makaminta na nukiliya tare da shirya kai hari da shi zuwa kasar Lithuania.

Rasha ta ce za ta zauna cikin shirin nufar Lithuania da makaman nukiliyarta idan ƙasar ta karɓi wasu makaman nukiliya daga tarin makaman ƙawayenta na kungiyar NATO a yankinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng