An Tafka Asara Mai Yawa da Gobara Ya Babbake Shaguna a Wata Kasuwa a Jihar Kano

An Tafka Asara Mai Yawa da Gobara Ya Babbake Shaguna a Wata Kasuwa a Jihar Kano

  • Wata mummunar gobara ta kone shaguna kusan 100 a kasuwar kayan hannu da na gida ta Kingsway da ke jihar Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:00 na dare ranar Alhamis kuma ta ci gaba da ci har zuwa safiyar Juma'a
  • Hukumar kashe gobara ta Kano ta ce tangardar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, wacce ta jawo asarar daruduwan miliyoyin Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - 'Yan kasuwar sayar da kayan gida ta Kingsway da ke kan titin Murtala Muhammad Way a jihar Kano sun tafka sara a wata mummunar gobara da ta auku.

Rahotanni sun nuna cewa gobara ta yi mummunar illa a shaguna tare kona kayayyaki masu dinbin yawa a kasuwar tsakanin daren jiya Alhamis zuwa safiyar yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta hana Katsina da wasu jihohin Najeriya yin sulhu da 'yan bindiga

Kasuwa.
Wani bangaren barnar da gobara ta yi a kasuwar Kingsway da ke cikin birnin Kano Hoto: Legit.ng
Source: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa kasuwar ta yi kaurin suna wajen sayar da kayan amfanin gida na hannu kamar firiji, na'urorin sanyaya iska, kafet, kofofi, kujeru, tebura da sauran kayayyaki.

Wadanda lamarin ya faru a idonsu sun ce wuta ta kama a kasuwar ne da misalin karfe 10:00 na dare jiya Alhamis, inda ta ci gaba da ci har zuwa safiyar Juma'a duk da kokarin da jami'an kwana-kwana suka yi na dakile ta.

An yi asarar miliyoyin Naira a Kano

Daya daga cikin yn kasuwar da wuta ta ci shagunansu, Kabiru Idris Muhammad, ya bayyana cewa Hukumar Kwana-Kwana ta Kano ta tura motoci fiye da 10 domin shawo kan lamarin.

Ya ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin gobarar ba, amma ya bayyana ta a matsayin mafi muni a tarihin kasuwar.

"Ba mu san musabbabin gobarar ba tukuna. Gobara ce mai tsananin muni kuma kadan daga cikin kayayyaki aka samu aka ceto, kusan komai ya kone," in ji shi.

Kara karanta wannan

Dalibai mata sun diro daga bene da wasu miyagu suka kai hari kwalejin lafiya a Najeriya

Ya kara da cewa wasu 'yan kasuwa sun yi asarar shaguna da dama, yayin da wasu kuma suka rasa dukkan hajojinsu.

"Babu dan kasuwar da zai iya fada maka yawan asarar da muka yi, amma kowa ya san magana ake ta daruruwan miliyoyin Naira. Kusan shaguna 100 ne suka kone," in ji shi.

Kabiru ya tabbatar da cewa gobarar ta shafi wani bangare na kamfanin jigilar kayayyaki na DHL, kana ya yi kira ga gwamnati da ta kai dauki cikin gaggawa ga yan kasuwarda suka yi asara.

An gano dalilin tashin gobara

Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar gobarar, tana mai cewa binciken farko ya ganocewa wutar lantarki ce ta haddasa kamawar wuta a kasuwar.

A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya fitar, ya ce funj aka tura yan kwana kwana daga hedikwata da sauran tashoshin birnin Kano zuwa wurin da lamarin ya faru.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa da isarsu, sun tarar da wani bene mai hawa daya da kuma wani babban fili na kasuwanci mai girman kafa 300 da 200 suna ci da wuta, cewar rahoton Remium Times.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wurin da dalibai ke yin jarabawar WAEC a Kogi

Hukumar ta ce gobarar ta lalata ofisoshi biyu, dakunan zama biyu, bayan gida biyu da kicin guda daya, tare da shaguna biyu da ke kasa na kamfanin TUSRAYS Nigeria Ltd.

Gobara ta yi barna a gidan Sarki

A wani rahoton, kun ji cewa wata gobara ta lalata gidan Sarkin Dawakin Zuba da ke karamar hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Alhaji Musa Danliman.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da ake kusa sun kai masa dauki yayin da wutar ta shi, amma duk da haka ta yi mummunar barna.

Bayanai sun nuna cewa tashin wutar ya jawo wa Alhaji Musa Danliman asarar dukiya mai dimbin yawa ta miliyoyin Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262