'Ya Raba Kafa'; Hadimin Gwamna Abba Ya Yi Tone Tone kan Kwankwaso

'Ya Raba Kafa'; Hadimin Gwamna Abba Ya Yi Tone Tone kan Kwankwaso

  • Mai magana da yawun Gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi maganganu kan siyasar Rabiu Musa Kwankwaso
  • Hadimin na Gwamna Abba ya zargi madugun na Kwankwasiyya da yi wa kansa butulci ta hanyar raba gari da jam'iyyar NNPP
  • Hakazalika, ya bayyana cewa Sanata Rabiu Kwankwaso yana raba kafa a tsakanin jam'iyyu, inda yake yi wa 'yan siyasa wayau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi maganganu kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa Kwankwaso yana yi wa sauran 'yan siyasa wayau, inda yake raba kafa tsakanin jam'iyyu.

Hadimin Abba ya yi zarge-zarge kan Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Sanusi Bature ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Dokin Karfe wadda aka sanya a shafin Facebook a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Me kuma suke so"; Ana neman tunzura jagoran NDC kan tikitin Obi da Kwankwaso a 2027

Me Kakakin Abba ya ce kan Kwankwaso?

Hadimin na Gwamna Abba ya tuna baya kan zaben 2023, inda ya ce Kwankwaso ya shiga zaben ne a wancan lokacin da jam'iyya biyu.

"A 2023 da jam'iyya biyu ya shiga zabe, sai da ya hallaka PDP ta kai matakin da kuri'a 15,000 kamar na kansila ta iya samu. Ya rike ta ya ce mata ita ce 'option A' sannan kuma yana NNPP".

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Hadimin Abba ya ce Kwankwaso ya ci amana

Hadimin na gwamnan Kano ya bayyana cewa Kwankwaso ya ci amanar kansa ta hanyar ficewa daga jam'iyyar NNPP.

"Kwankwaso a karan kansa ya bar NNPP, barin NNPP da ya ce cin amana ne, shi da kansa sai ya ci amanar kansa da kansa, ya yi wa kansa butulci. Sai ya bar NNPP ya kuma ajiye yaransa a cikinta."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Kwankwaso ya raba kafa a ADC

'Dan siyasar ya yi zargin cewa bayan Kwankwaso ya shiga jam'iyyar ADC, ya raba kafa ta hanyar rika magana da David Mark da Nafiu Bala Gombe.

Kara karanta wannan

"Suna da amfani": Jagoran NDC ya fadi makomar Kwankwasiyya da Obidents a jam'iyyar

"Da ya shiga ADC nan ma sai ya raba kafa, yana magana da David Mark, da ake karbarsa ma David Mark ne ya zo ya karbe shi, amma kuma a karkashin kasa yana tare da Nafiu Gombe."
"Da rana yana tare da David Mark a fili da daddare kuma yana tare da Nafiu Gombe a kan waya har asuba. Ka ga ADC din ma da ya shiga sai ya raba kafa, yana tare da nan yana tare da nan."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Zuwa yanzu Kwankwaso bai tanka wadannan zarge-zarge ba, kuma Dawakin Tofa bai kawo hujjojin da suka tabbatar da wadannan batu ba.

Sanusi Bature ya yi magana kan Kwankwaso
Sanusi Bature Dawakin Tofa a wurin taron jam'iyyar APC Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi maganar sake hadewa da Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan yiwuwar sake hadewa da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.

Kwankwaso ya bayyana cewa ba korar Abba Kabir Yusuf ya yi ba a tafiyar Kwankwasiyya, shi gwamnan da kansa ne ya tafi ba tare da izinin shi ba.

'Dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar NDC a zaben 2027, ya bayyana cewa a shriye ya ke ya yafe wa duk wani dan Kwankwasiyya da aka samu sabani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng