Shugaba Trump Ya Ragargaji Iran duk da Shirin Kulla Yarjejeniya
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kausasa harshe kan mahukunta a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batun yarjejeniya
- Donald Trump ya karyata abin da a cewarsa mahukunta a Iran ne suka tseguntawa kafafen yada labarai kan yarjejeniyar da za a kulla
- Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa ko kadan ba su da dadin harka wajen kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Duk da ayyana cewa an kusa kammala yarjejeniya da Iran, Shugaba Donald Trump ya yi Allah-wadai da mahukunta a ƙasar Iran.
Shugaba Donald Trump ya siffanta su da “marasa daraja” saboda abin da ya kira bayanan ƙarya game da batun yarjejeniyar.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Juma'a, 12 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran
Kalaman Shugaba Trump na zuwa ne bayan ya nuna alamar cewa an kusa cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, domin kawo karshen yaki.
Meyasa Donald Trump ya ragargaji Iran?
Shugaba Trump ya soki Iran ne kan tseguntawa kafafen yada labarai bayanai dangane da yarjejeniyar da za a kulla.
Trump ya nuna cewa abubuwan da aka tseguntawa kafafen yada labaran, ba su da wata alaka da sharuddan da aka amince da su a rubuce.
“Sharuddan da Iran ta tseguntawa kafafen yaɗa labaran karya ba su da wata alaka da sharuddan da aka amince da su a rubuce. Abin da suka faɗa, har da bayanansu mai rauni da ban takaici kan cewa an ƙulla yarjejeniya, ba shi da alaƙa da gaskiya."
"Mutane ne marasa daraja sosai wajen yin harka da su. Tare da su, babu wani abu wai shi yin harka da kyakkyawar manufa. Abin mamaki!"
"Haka kuma, harin jirage marasa matuka da suka kai a daren jiya wanda aka fatattaka a kan jiragen ruwan Indiya da ke barin mashigar Hormuz gaba ɗaya abin da za a amince da shi ba ne. Gara su gyara halinsu, kuma cikin gaggawa!"
- Shugaba Donald Trump

Source: Facebook
Abin da aka ce kan batun yarjejeniyar
Jaridar Tribune ta ce kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun bayar da rahoton daki-daki na yarjejeniyar a farkon ranar Juma'a, 12 ga watan Yunin 2026.
Cikin abubuwan da suka bayyana har da ƙin amincewar Iran na miƙa ikon mashigar Hormuz da kuma buƙatar yarjejeniyar na sakin dalar Amurka tiriliyan 24 na kuɗin kasar da aka rike.
Trump ya dakatar da kai hari a Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da soke shirin kai hare-haren da aka tsara a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya bayyana cewa ya soke kai hare-haren ne bayan ci gaban da aka samu a tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban kasar na Amurka ya nuna alamun yiwuwar sanyawa wata yarjejeniya hannu da mahukunta a Tehran bayan tattaunawa ta kai matakin ƙoli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
