Ana Neman Hana Pantami Shiga Sabon Zaben Fitar da Gwani na PDP a Gombe
- PDP ta ce za a gudanar da sabon zaɓen fidda gwamnan Gombe yau Talata, bayan kotu ta soke sakamakon zaɓen fidda gwani na baya
- Jam’iyyar ta ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Usman Aliyu Garry da Khamisu Ahmed Mailantarki ne aka tantance domin shiga sabon zaɓen
- Garry ya ƙalubalanci sanya Pantami, yana cewa bai cikin jerin ’yan takarar da PDP ta gabatar wa INEC kafin ya shiga jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Bangaren jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Gombe da ke samun goyon bayan tsohon Gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa za a gudanar da sabon zaɓen fidda ɗan takarar gwamna yau Talata, 29 ga Satumba, 2026.
Jam’iyyar ta ce an tantance ’yan takara uku domin shiga sabon zaɓen, wato tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami; Usman Aliyu Garry; da Khamisu Ahmed Mailantarki.

Source: Facebook
Sakataren Yaɗa Labarai na wannan ɓangaren PDP na jihar, Abdulkadir Ahmed Dukku, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waya da jaridar Leadership ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026.
PDP ta ce za ta bi umarnin kotu
Dukku ya ce za a gudanar da sabon zaɓen ne bisa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Gombe.
Kotun ta soke sakamakon zaɓen fidda gwani na baya wanda ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan Gombe a babban zaɓen 2027.
Garry ya ƙalubalanci shigar Pantami
Sai dai Usman Aliyu Garry, wanda ya ƙalubalanci zaɓen fidda gwani na baya da ya haifar da zaɓen Pantami, ya nuna adawa da shigar Pantami cikin sabon zaɓen na yau.
Garry ya ce ya kamata a takaita sabon zaɓen ga ’yan takarar da suka cancanta bisa tanadin hukuncin kotu, yana mai dagewa cewa bai kamata a bar Pantami ya shiga takarar ba.

Kara karanta wannan
INEC na da 'yan takara ko jam'iyyar da take goyon baya a zaben 2027? An samu bayanai
Da yake magana da ’yan jarida a Gombe ranar Litinin, Garry ya ce kwamitin tantance ’yan takarar da tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya jagoranta, ya riga ya tantance masu neman tikitin gwamnan jam’iyyar.
Garry ya ce an hana wasu shiga zaɓen farko
A cewar Garry, an hana wasu daga cikin masu neman takarar damar shiga zaɓen fidda gwani na farko, lamarin da ya sa suka garzaya kotu domin neman hakkinsu.
Ya ce shi da wasu ’yan takara sun rubuta wa shugabannin PDP da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), inda suka nemi a hana Pantami shiga sabon zaɓen.
Garry ya kafa hujjar tasa ne kan fahimtarsa cewa ba a saka sunan Pantami cikin jerin masu neman tikitin gwamnan da PDP ta miƙa wa INEC ranar 10 ga Mayu ba.
Garry ya ce Pantami ya shiga PDP daga baya
“Pantami ya shiga PDP ne ranar 19 ga Mayu, kuma kotu ma ta tabbatar da hakan. Saboda haka, ba a saka sunansa cikin jerin ’yan takarar jam’iyyar da aka miƙa wa INEC ba."
“Bai kamata a bar shi ya shiga sabon zaɓen fidda gwani ba,” in ji Garry.
Ya yi kira ga PDP da INEC da su tabbatar da cewa an gudanar da sabon zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke.

Source: Facebook
Sakon Sanata Goje ga magoya bayansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya aika sako ga magoya bayansa kan zaben 2027.
Sanata Goje ya umurci magoya bayansa da kada su zaɓi mutanen da suka yi aiki wajen hana shi samun tikitin komawa Majalisar Dattawa.
Asali: Legit.ng

