Bayan Matsalolin da Aka Samu, Shugaban Hukumar Bogi Ta PFIPC Ya Bayyana a gaban Kotu

Bayan Matsalolin da Aka Samu, Shugaban Hukumar Bogi Ta PFIPC Ya Bayyana a gaban Kotu

  • Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙira da gudanar da wata hukuma ta bogi, ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
  • Ana tuhumar Adeyemi da laifukan ƙulla makirci, ƙirƙirar takardu da yin kwaikwayon wani wanda ya saba wa doka
  • ’Yan sanda sun ce sun gano asusun banki 34 da ke da alaƙa da Adeyemi, ciki har da tara da aka buɗe da sunayen hukumomin gwamnati na bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙira da gudanar da wata hukuma da ya yi ikirarin cewa ta gwamnati ce, ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

An gurfanar da Adeyemi, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban hukumar PFIPC da aka gano ta bogi ce domin fara shari’a, bayan ƙoƙarin gabatar da shi gaban kotun ya sha faskara.

Kara karanta wannan

2027: Rarara ya sake fitowa da maganganu masu zafi kan 'yan Arewa da Tinubu

Adeyemi.
Shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Prince Adeniyi Adeyemi Hoto: Prince Adeniyi Adeyemi
Source: Facebook

An gurfanar da Adeyemi a gaban kotu

Premium Times ta rahoto cewa an shigar da Mista Adeyemi cikin kotun da misalin ƙarfe 2:33 na rana yau Laraba, sanye da doguwar farar riga da kuma hular baseball fara.

Wata jami’ar ’yan sanda ta sashen NPF-NCCC ce ta raka shi zuwa cikin kotun. Ko da yake ya bayyana cikin fara’a, amma dukar da kansa ƙasa, yayin da gefen hularsa ya ɗan rufe fuskarsa, yana jiran a kira shari’arsa.

Yadda aka gaza gurfanar da Adeyemi

Bayyanarsa a kotun ta zo ne bayan ƙoƙarin gurfanar da shi da dama tun bara ya ci tura saboda dalilai daban-daban, ciki har da buƙatun lauyoyinsa, rashin zuwansa kotu da sauransu

An sanya shari’ar cikin jadawalin shari'o'in babbar kotun tarayya na ranar 3 ga watan Fabrairu domin gurfanar da shi, amma ba a gudanar da zaman ba.

An shigar da ƙarar ne a watan Nuwamba 2025, bayan da ’yan sanda suka kama Mista Adeyemi a watan Oktoba na wannan shekarar, biyo bayan wata ƙara da Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ya shigar.

Kara karanta wannan

Matsin da ake ciki yana damun Tinubu, ya fadi hanyar tsame mutane miliyan 5 daga talauci

’Yan sanda sun tuhumi Adeyemi da wasu mutane biyu, Femi da Anu, waɗanda aka ce suna can a ɓoye. An tuhume su da laifuka takwas da suka haɗa da ƙulla makirci, ƙirƙirar takardu da yin kwaikwayon wani.

Takardun da ake zargin an ƙirƙira

A tuhume-tuhume na ɗaya, biyu, uku, huɗu, shida, bakwai da takwas, masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa Mista Adeyemi da sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa baki wajen ƙirƙirar wasu takardun hukuma.

Takardun sun haɗa da wata takardar nadin aiki da ake zargin Shugaban Ƙasa ya sanya hannu, amincewar fara aiki da ake zargin an tura ga PFIPC, buƙatun amincewa da buɗe asusun ma’aikata da samar da ofishin aiki.

Adeyemi.
Prince Adeniyi Adeyemi lokacin da ya isa harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: @ImranMuhd
Source: Twitter

A tuhuma ta biyar, masu gabatar da ƙara sun zargi Adeyemi da gabatar da kansa a matsayin Darakta-Janar na PFIPC, laifin da ake hukuntawa ƙarƙashin Sashe na 179 na Penal Code.

Masu binciken ’yan sanda sun ce sun gano wasiƙun sadarwa tsakanin hukumar da ake zargin ta bogi da wasu hukumomin gwamnati, tare da gano asusun banki 34 da ke da alaƙa da Mista Adeyemi.

Gbajabiamila ya maka Adeyemi a kotu

Kun ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya maka shugaban hukumr bigi, Adeniyi Adeyemi a gaban kotu.

Gbajabiamila ya bukaci kotu ta umarci Adeyemi ya janye kalaman da ake zargi da bata suna tare da neman afuwa a jaridu, sannan ya biya shi diyyar Naira biliyan 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262