Atiku Ya Yi Martani kan Rasuwar Manjo Janar Rabe a Hannun 'Yan Bindiga

Atiku Ya Yi Martani kan Rasuwar Manjo Janar Rabe a Hannun 'Yan Bindiga

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna takaicinsa kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar a hannun 'yan bindiga
  • Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar marigayin a hannun 'yan bindiga a matsayin abin bakin ciki wanda ba za a amince da shi ba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce rasuwar ta nuna yadda matsalar rashin tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) hannun 'yan bindiga.

Atiku ya ce mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe a hannun 'yan bindiga da kuma sabon harin ta'addanci da aka kai a kauyukan Chibok da ke jihar Borno, alama ce ta Najeriya tana ci gaba da rasa nasarorin da ta samu da ƙyar a yaƙi da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

Atiku ya yi magana kan rasuwar Rabe Abubakar
Atiku Abubakar na jawabi a wajen wani taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Atiku ya fitar ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026 wadda Paul Ibe, ya wallafa a shafinsa na X.

Me Atiku ya ce kan rasuwar Rabe Abubakar?

Atiku ya siffanta mutuwar tsohon daraktan na hulɗa da jama'a na ma'aikatar tsaro a matsayin abin takaici da ke nuna gazawar gwamnatin tarayya wajen kare 'yan ƙasa, inda ya gargaɗi cewa babu ɗan Najeriya da ke cikin aminci a ƙarkashin halin tsaro na yanzu.

Yayin da yake mayar da martani kan rasuwar, Atiku ya ce mutuwar babban jami'in soja mai ritaya a hannun masu laifi abin takaici ne kuma abu ne da ba za a amince da shi ba.

“Janar Rabe ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Najeriya. Ya yi wa wannan ƙasa aiki cikin girma, jajircewa, da ƙwarewa. Ganin irin wannan mutumin zai iya rasa rayuwarsa a hannun masu laifi abu ne mai sosai zuciya kuma ba za a amince da shi ba."

Kara karanta wannan

NDC ta yi martani kan batun Kwankwaso ya yi barazanar barin jam'iyyar

- Atiku Abubakar

Atiku ya koka kan rashin tsaro

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, lamarin yana fallasa yadda 'yan Najeriya ke ƙara kasancewa cikin haɗari kuma yana nuna gazawar tsarin tsaron ƙasar.

“Mutuwarsa fama mana wani babban rauni mai raɗaɗi kan tsarin tsaron ƙasarmu da kuma babbar tunatarwa na cewa hatta shugabanninmu na soja suna cikin haɗari 'yan ta'adda da suka addabi kasar."

- Atiku Abubakar

Atiku ya koka kan rashin tsaro a Najeriya
Atiku Abubakar tare da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: @atiku
Source: Twitter

​Atiku ya ce miyagu na kara karfi

Ya jaddada cewa wannan bala'i ya wuce mutuwar jami'in soja mai ritaya guda ɗaya, hakan yana nuna babban rikicin ƙasa baki ɗaya inda ƙungiyoyin masu laifi ke ƙara samun ƙarfin gwiwa.

“Halin da Janar Rabe ya tsinci kansa a ciki ba kansa ya fara aukuwa ba. A lokutan baya-bayan nan, wasu manyan jami'an soja da sanannun 'yan Najeriya ko dai an kashe su ko kuma an sanya su a fuskanci abubuwa mara dadi a hannun ƙungiyoyin masu laifi."

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga

"Saƙon da ake tura wa yana da haɗari: cewa waɗanda suka taɓa kare ƙasar ba za su iya dogaro da ƙasar don samun kariya ba."

- Atiku Abubakar

Tinubu ya yi magana kan rasuwar Rabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) a hannun 'yan bindiga.

Shugaban Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, musamman matarsa wadda take a hannun masu garkuwar.

Hakazalika, shugaban kasar na Najeriya ya jajanta wa gwamnatin jihar Katsina da rundunar sojojin Najeriya bisa wannan babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com