‘Babban Kuskuren da Yan Najeriya Za Su Yi kan Rashin Sake Zaben Tinubu’

‘Babban Kuskuren da Yan Najeriya Za Su Yi kan Rashin Sake Zaben Tinubu’

  • Wani tsohon soja a Najeriya ya ce rashin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 zai zama babban kuskure
  • Ya ce gyare-gyaren gwamnatin Tinubu sun taimaka wajen inganta ilimi, yayin da NELFUND ke tallafa wa ɗalibaI
  • Kungiyar Renewed Hope Project 2027 ta ƙara burinta zuwa kuri’u miliyan 12, yayin da ake shirin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Wani Janar na Sojin Najeriya mai ritaya, Manjo Janar Abdulmalik Jibrin, ya bayyana rashin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 a matsayin “babban kuskure.

Tsohon sojan ya bukaci ’yan Najeriya su mara wa shugaban baya domin ya sake mulki na tsawon shekaru huɗu saboda samun karin ci gaba.

An fadi illar rashin zaben Tinubu a 2027
Shugaba Bola Tinubu yayin taron majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Jibrin ya yi wannan magana ne a Abuja yayin wani tattakin ɗalibai miliyan ɗaya da aka shirya domin nuna goyon baya ga Tinubu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci

'Amfanin sake zaben Tinubu a 2027'

Ya ce ci gaba da mulkin Tinubu ya zama dole domin dorewar abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da ake samu sakamakon sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa.

Jibrin ya ce:

“Zai zama babban kuskure ga ’yan Najeriya idan ba mu sake ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar mulkar ƙasar nan na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.”
An fadi amfanin sake zaben Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yayin ziyara a Lagos. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Source: Twitter

Zaben Tinubu: Shawarar da aka ba al'umma

Jibrin ya bukaci magoya baya da ƙungiyoyin farar hula su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna abin da ya bayyana a matsayin ƙwarin gwiwa wajen kula da jin daɗin ɗalibai da samar da damar samun ilimi.

A cewarsa, tallafin da aka bai wa manyan makarantu ya taimaka wajen faɗaɗa su, kafa sababbin tsangayu da ƙarfafa ilimin fasaha da koyar da sana’o’i.

Dangane da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND, Jibrin ya ce shirin ba da lamunin ɗalibai yana taimaka wa ɗaliban da iyalansu ba za su iya ɗaukar nauyin karatun manyan makarantu ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Zan iya yanke hannuna saboda ba Tinubu kuri'u miliyan 2.5': Wani shugaban APC

Ya ce:

“Za ku yarda da ni idan kuka kalli tituna, za ku ga yara da yawa da ya kamata su kasance a makarantu, amma sun daina zuwa saboda iyayensu ba su da kuɗin biyan kuɗin karatunsu.”

Ya ƙara da cewa NELFUND na bayar da lamunin karatu ba tare da ruwa ba ga ɗaliban da suka cancanta domin biyan kuɗin makaranta da kuma bukatun rayuwa.

Tinubu ya magantu bayan dura a Najeriya

An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa game da lafiyarsa bayan komawarsa Najeriya daga hutun aiki a Turai.

Tinubu ya ce babu wata matsala da ke damunsa, yana mai bayyana kansa a matsayin mai lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki.

Shugaban ya dawo Najeriya ne ranar Talata bayan shafe kusan mako huɗu a Turai, inda ya fara zama a Landan kafin ya koma Paris a Faransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.