An Tura Sojoji Bataliya Bataliya Zamfara Su Gwabza da 'Yan Bindiga

An Tura Sojoji Bataliya Bataliya Zamfara Su Gwabza da 'Yan Bindiga

  • Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin soji uku a jihar Zamfara domin ƙarfafa ayyukan tsaro da gaggauta tunkarar barazanar tsaro
  • Sababbin bataliyoyin sun haɗa da 12 Infantry Battalion da aka kafa a Bakura, 23 Infantry Battalion a Kaura Namoda da 28 Infantry Battalion a Anka
  • Rundunar ta ce sabbin rundunonin za su faɗaɗa ayyukanta tare da inganta tsaron yankunan da aka ba su alhakin kulawa da su a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Zamfara – Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin sojoji uku a jihar Zamfara domin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta gaggawar mayar da martani ga barazanar tsaro.

Sabbin bataliyoyin su ne 12 Infantry Battalion da ke Bakura, 23 Infantry Battalion da ke Kaura Namoda da 28 Infantry Battalion da ke Anka.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sabon rikici ya barke a Taraba, rayuka sun salwanta

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu sojojin Najeriya a cikin daji. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Dalilin tura bataliyoyi Zamfara

Punch ta rahoto cewa rundunar ta ce sabbin bataliyoyin za su faɗaɗa wuraren da sojoji ke gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da tsaron yankunan da aka ba kowacce bataliya alhakin kulawa.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da rundunonin, Kwamandansu, Kanar Joseph Umaru, wanda ya wakilci Kwamandan Rundunar Sojoji ta 8, Manjo Janar BP Koughna, ya ce rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan tsaro a Zamfara.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da kare al’ummar da ke bin doka, yana mai cewa samun zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwar jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da al’ummomi.

Kiran sojoji ga jama'a

Kanar Umaru ya buƙaci mazauna jihar su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanan sirri masu inganci, sahihai kuma masu amfani a kan lokaci.

Ya kuma shawarci sojojin da aka tura sababbin bataliyoyin da su kiyaye doka, ƙwarewar aiki da sanya ido a yayin gudanar da ayyukansu, tare da bin ƙa’idojin amfani da ƙarfi da aka tanada.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Sarakunan Zamfara sun yi maraba

Sarakunan Bakura, Anka da Kaura Namoda sun yi maraba da kafa sababbin bataliyoyin, tare da yabawa Rundunar Sojin Najeriya kan ƙara yawan jami’an tsaro a yankunansu.

Sarkin Bakura, Alhaji Bello Sani; Emir na Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad; da Sarkin Kaura Namoda, Manjo Dokta Sanusi Mohammed Ahmed (mai ritaya), sun ce matakin zai taimaka wajen inganta tsaro a al’ummomin jihar.

Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal a wajen taron tsaro. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Sarakunan sun kuma tabbatar wa rundunar cewa masarautunsu za su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai, musamman wajen wayar da kan jama’a da musayar bayanan sirri.

An yankewa sojoji wuta a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NUEE) a jihar Bauchi ta yi barazanar katse wutar lantarki saboda zargin cin zarafin wasu daga cikin mambobinta da jami’an Rundunar Sojin Sama ta Najeriya suka yi.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Rilwanu Shehu, ya bayyana hakan ne yayin wata zanga-zangar lumana da ma’aikatan suka gudanar a Bauchi.

Shehu ya ce zanga-zangar ta biyo bayan zargin mamaye ofishin ayyukan JEDC da ke Bauchi da wasu jami’an tsaro suka yi a ranar 18 ga Satumba, inda aka zargi ma’aikatan da yanke lantarki daga wasu wuraren Rundunar Sojin Sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng