'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Kebbi, an Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Kebbi, an Kashe Bayin Allah

  • Hatsabiban 'yan bindiga sun kai kazamin hari a wani kauyen jihar Kebbi wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane da dama
  • Gwamnatin jihar ta jajanta kan harin tare da mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan mutanen da suka rasa 'yan uwansu a mummunan harin
  • Hakazalika ta kara tabbatar da alkawarinta na ganin ta kare rayuka da dukiyoyin mutane daga hare-haren 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - 'Yan bindiga dauke da makamai sun hallaka aƙalla mutane 20 a wani mummunan hari da suka kai a jihar Kebbi.

'Yan bindigan sun kashe mutanen ne a wani hari da suka kai a garin Fesken Rafi da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun yo barna a jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris na jawabi a wajen taro Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamnatin Kebbi ta yi jaje kan harin 'yan bindiga

Jaridar The Punch ta ce gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana matsanancin alhini game da lamarin, inda ta bayyana harin a matsayin abin takaici, sannan ta mika saƙon ta'aziyya ga iyalai da mazauna garin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Mutane sun huta, jami'an tsaro sun yi ajalin hatsabibin dan bindiga, Baccujo

Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Tafida ya bayyana hakan yayin da yake jagorantar wata babbar tawagar gwamnati a ziyarar ta'aziyya ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.

Gwamnati ta dauki alkawarin kare al'umma

Sanata Umar Tafida ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati tana nan daram kan alƙawarinta na magance rashin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.

Ya sanar da cewa za a tura ƙarin jami'an tsaro da kayayyakin aiki zuwa yankin domin ƙarfafa ayyukan tsaro, dawo da zaman lafiya, da kuma hana aukuwar hare-hare a nan gaba, Daily Post ta kawo rahoton.

“Muna tare da ku a cikin wannan baƙin ciki kuma muna nan daram kan alƙawarinmu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin Jihar Kebbi."

- Sanata Umar Tafida

An jinijina wa Gwamnatin jihar Kebbi

Shugaban karamar hukumar Arewa, Sani Tela, da kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Arewa a majalisar dokoki ta jihar Kebbi, Nuradeen Kangiwa, sun shaida wa tawagar cewa harin ya auku ne 'yan kwanaki da suka gabata kuma ya yi sanadiyyar asarar rayuka masu yawa.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Kaduna, an kashe manyan jagorori 4

Sun jinjina wa Gwamna Nasir Idris saboda ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na yaƙi da rashin tsaro da kuma saurin kawo dauki ga halin da al'ummomin da abin ya shafa ke ciki.

'Yan bindiga sun kashe mutane a jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugabannin gargajiya, ciki har da Dikkon Kabi, Alhaji Kabiru Sulaiman, wanda ya wakilci Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, da kuma Hakimin Bui, Alhaji Abubakar Dan-Malam, su ma sun yaba da saƙon gwamnatin.

Sarakunan sun yi kira da a gina hanyar da za ta haɗa al'ummar Fesken Rafi da babban titi, inda suka lura cewa samar da hanya mai kyau zai taimaka wa jami'an tsaro wajen kai ɗauki cikin sauri, sauƙaƙa ayyukan tattalin arziki, da kuma inganta yanayin rayuwar mazauna yankin.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa waau hatsabiban 'yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro na 'yan sa-kai a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe jami'an tsaron na 'yan sa-kai ne guda biyu a garin Ta-Hoss da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Kisan dakarun na sa-kai guda biyu ya tsananta fargaba a yankin, inda mazauna garin ke nuna fargaba game da ci gaban ƙalubalen tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng