NDC Ta Yi Martani kan Batun Kwankwaso Ya Yi Barazanar Barin Jam'iyyar

NDC Ta Yi Martani kan Batun Kwankwaso Ya Yi Barazanar Barin Jam'iyyar

  • Jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta yi tsokaci kan batun Sanata Rabiu Musa Kwamkwaso ya yi barazanar ficewa daga cikinta
  • NDC ta bayyana cewa babu abokan hamayya na siyasa na kokarin rura wutar rikici a cikinta domin nuna son rai
  • Sakataren yada labarai na NDC na kasa ya bayyana cewa sabani ba bakon abu ne a jam'iyyun siyasa, musamman ma a wadda take sabuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar NDC ta yi martani kan batun barazanar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta ficewa daga cikinta.

NDC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ɗan takararta na mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi barazanar barin jam'iyyar saboda saɓani game da tsayar da 'yan takara a jihar Kano.

NDC ta yi magana kan barazanar Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na NDC na kasa, Osa Director, ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Arise News a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Me kuma suke so"; Ana neman tunzura jagoran NDC kan tikitin Obi da Kwankwaso a 2027

Shin Kwankwaso ya yi barazanar barin NDC?

Osa Director ya siffanta iƙirarin a matsayin “hasashe da jita-jitar kafafen yaɗa labarai” da nufin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Sakataren yada labaran na NDC na kasa, ya jaddada cewa Kwankwaso bai taɓa tunanin barin jam'iyyar ba.

“Babu wani lokaci da jagoranmu, Kwankwaso, ya yi barazanar barin jam'iyyar. Waɗancan kawai hasashe ne da jita-jitar kafafen yaɗa labarai da ke ƙoƙarin ɓata sunan jam'iyyar, kuma mun san daga inda suke fitowa."

- Osa Director

Su waye ke rura wuta a NDC?

A cewarsa, abokan hamayyar siyasa da wasu masu son rai ne ke rura wutar rahotannin don nuna kamar akwai rikici a cikin jam'iyyar.

Kalaman nasa sun biyo bayan rahotannin da ke alaƙanta Kwankwaso da rashin gamsuwa kan wasu canje-canje da aka yi a jerin sunayen 'yan takarar jam'iyyar na jihar Kano.

Rigimar ta barke ne bayan da NDC ta sauya wasu 'yan takara da tun farko ƙungiyar Kwankwasiyya ta gabatar, wadda ita ce kungiyar siyasa mai biyayya ga tsohon gwamnan na jihar Kano.

Kara karanta wannan

NDC ta ce an samu kura kurai a zaben fitar da gwani, ta nemi afuwa

NDC ta yi martani kan barazanar da aka ce Kwankwa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sai dai, jami'an jam'iyyar sun dage cewa ba a yi wata barazana makamanciyar hakan ba, kuma ana nan ana ci gaba da tuntuɓar juna domin magance duk wata damuwa da ta taso daga tsarin zaɓen 'yan takarar.

Director ya ce saɓani kan takara ba baƙon abu ba ne a jam'iyyun siyasa, musamman ma a cikin ƙungiyar haɗaka da ke haɓaka wadda take shirin shiga babban zaɓe.

An bukaci Kwankwaso ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a APC, Faizu Alfindiki, ya yi kira ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya hakura da jam'iyyar NDC.

Fa'izu Alfindiki ya bayyana cewa APC ce ta rage wa Kwankwaso a matsayin jam'iyyar da zai yi tasiri gabanin babban zaben shekarar 2027.

Ya ce cece-kucen da suka dabaibaye zaɓen fitar da gwani a NDC sun sa tilas Kwankwaso ya sake nazarin makomarsa ta siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng