Trump Ya Ballo Ruwa, 'Yan Majalisa Sun Bude Masa Wuta kan Shirin Yarjejeniya da Iran

Trump Ya Ballo Ruwa, 'Yan Majalisa Sun Bude Masa Wuta kan Shirin Yarjejeniya da Iran

  • Alamu sun nuna Amurka da Iran na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin da suke yi a tsakaninsu
  • 'Yan majalisar jam'iyyar Democrat sun soki Shugaba Trump kam yarjejeniyar wadda aka shirin kullawa a tsakanin bangarorin
  • Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa yarjejeniyar ba komai ba ce fa ce mika wuya ga bukatun Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - 'Yan majalisa na jam'iyyar Democrats sun nuna shakku game da yarjejeniyar zaman lafiya da ake kyautata zaton kullawa tsakanin Shugaba Donald Trump da Iran.

Sanata Adam Schiff ya bayyana cewa a baya sun saba jin hakan, amma kuma sai lamarin yaki tabbata.

'Yan Democrat sun ragargaji Donald Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump zaune a ofis Hoto: Mandel Ngan
Source: Getty Images

Sanatan mai wakiltar California ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya ragargaji Iran duk da shirin kulla yarjejeniya

Sanata a Amurka ya soki Donald Trump

Ya nuna cewa Shugaba Trump ya sha saba tarin alkawura kan yakin da Amurka take yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

“Shugaban kasa ya ce yaƙin ya ƙare. Ina fata yana da gaske yake yi. Amma mun sha jin hakan a baya. Tare da tarin alƙawuran da aka saba.”
“Ya zama musabbabin yaƙe-yaƙe, amma bai rage kuɗaɗen da ake kashewa ba. Kuma hakan ya cutar da al'ummar Amurka ƙwarai da gaske."

- Adam Schiff

An caccaki Trump kan yarjejeniya da Iran

Shi kuwa ɗan majalisa Seth Moulton, ya siffanta yiwuwar yarjejeniyar a matsayin “asalin takardar mika wuya”, tashar Aljazeera ta kawo labarin.

“Wannan mummunar yarjejeniya ce!. Ainihin takardar mika wuya ce daga Donald Trump zuwa ga babban jagoran Iran."
"Ma'ana, dalar Amurka biliyan 100 na kuɗin masu biyan haraji da aka riga aka zuba a wannan yaƙin, 'yan Amurka 14 da suka mutu, sannan mu samu yarjejeniyar da kawai za ta sake buɗe mashigar da take ma a buɗe take kafin ya fara wannan wawan yaƙin. Ta yaya wannan zai zama nasara?”

Kara karanta wannan

Trump ya dakatar da sojojin Amurka daga kai hari a Iran bayan samun gargadi

- Seth Moulton

An taso Trump a gaba kan yarjejeniya da Iran
Shugaba Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Yan jam'iyyar Republican sun soki Iran

Sanata na jam'iyyar Republicans Ron Johnson ya bayyana a cikin wani bidiyo da kafar Iran International ta wallafa cewa samun makamin nukiliya da Iran za ta yi zai zama “barazana ga wanzuwar” Amurka.

Ya bayyana fatan cewa Trump zai yi nasarar hana hakan, kuma ya ce:

“Ya kamata a watsar da Ayatollahs na Iran a cikin kwandon shara na tarihi.”

John James, ɗan majalisa na jam'iyyar Republicans, ya bayyana cewa yana “cikin murna da zumuɗi” na ganin abin da zai fito daga yiwuwar yarjejeniyar Amurka da Iran, kuma ya ce matsin lambar Trump ne ya tilasta wa birnin Tehran zama a teburin tattaunawa.

Trump ya yi tir da mahukuntan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, ya ragargaji mahukunta a Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batun yarjejeniya.

Shugaba Donald Trump ya bayyana su da “marasa daraja” saboda abin da ya kira bayanan ƙarya game da batun yarjejeniyar.

Trump ya nuna cewa abubuwan da aka tseguntawa kafafen yada labaran, ba su da wata alaka da sharuddan da aka amince da su a rubuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng