Mutane Sun Gagara Amfani da Facebook, Instagram da Kamfanin Meta Ya Samu Matsala

Mutane Sun Gagara Amfani da Facebook, Instagram da Kamfanin Meta Ya Samu Matsala

  • Miliyoyin masu amfani da Facebook da Instagram sun fuskanci matsalar shiga da aika sakonni a sassa daban-daban na duniya
  • Rahotanni daga Downdetector sun nuna cewa korafe-korafe sama da 80,000 sun shiga yayin da matsalar ta shafi Messenger da Instagram
  • Har zuwa lokacin hada rahoton nan, kamfanin Meta bai bayyana musabbabin matsalar ba ko lokacin dawo da ayyukan gaba daya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Miliyoyin mutane a sassa daban-daban na duniya sun fuskanci tangarda bayan Facebook da Instagram sun samu matsalar aiki a ranar Alhamis.

Rahotanni sun nuna cewa matsalar ta kuma shafi Facebook Messenger, inda mutane suka ce sun kasa shiga shafukansu, duba abubuwa da kuma aika ko karbar sakonni.

Facebook da Instagram sun samu matsala a sassan duniya.
Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg da tambarorin Facebook, Instagram da WhatsApp. Hoto: The Asahi Shimbun / Contributor
Source: Getty Images

Fiye da mutane 80,000 sun yi korafi

Yayin da matsalar ta ci gaba, mutane da dama sun garzaya shafukan da ke bibiyar matsalolin yanar gizo domin tabbatar da ko matsalar ta shafi sauran mutane a duniya, in ji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

Bayanan da shafin Downdetector ya fitar sun nuna cewa korafe-korafe da suka shafi Instagram da Facebook sun karu sosai yayin matsalar.

Rahoton ya nuna cewa an samu sama da korafe-korafe 80,000 a lokacin da matsalar ta kai kololuwa.

Masu korafin sun bayyana matsaloli daban-daban da suka hada da kasa shiga shafukansu, makale wa a shafin 'loading' da kuma jinkirin aika sakonni.

Wasu mutane sun ce sun samu damar amfani da wasu sassan manhajojin, yayin da wasu suka fuskanci matsalar yankewar sadarwa.

Mutane sun bayyana abin da suka gani

Matsalar ta shafi masu amfani da wayoyi da kwamfuta, duk da cewa yadda matsalar ta afku ya bambanta daga wuri zuwa wuri, cewar rahoton Punch.

Wasu masu amfani da Instagram sun ce sun iya amfani da wasu bangarorin manhajar, amma sun kasa sabunta bangaren ganin rubutun mutane ko wallafa sababbin abubuwa.

Meta bai yi bayani kan matsalar ba

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kamfanin Meta wanda ya mallaki Facebook da Instagram da Messenger bai fitar da cikakken bayani kan musabbabin matsalar ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan fansho sun yi da na sanin tara wa gwamna kudin sayen fam

Har yanzu kamfanin Meta bai yi bayani game da musabbabin faruwar tangarda a Facebook da Instagram ba.
Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta. Hoto: Nathan Howard / Stringer
Source: Getty Images

Ana sa ran kamfanin zai gudanar da bincike yayin da rahotanni daga yankuna daban-daban ke ci gaba da bayyana.

Matsalar ta zama babban batu a yanar gizo, inda mutane suka fara tattauna muhimmancin dandalin Meta wajen sadarwa, kasuwanci da nishadi ga miliyoyin mutane a duniya.

Har yanzu dai mutane na ci gaba da fuskantar matsaloli mabambanta wajen amfani da Facebook da Instagram da Messenger yayin da suke jiran sanarwar Meta kan abin da ya haddasa tangardar.

Hajara Adam Muhammad, ta shaida wa Legit Hausa cewa:

“Instagram dina yana rufewa da kan shi duk lokacin da na bude shi. Da farko na yi tunanin matsalar wayata ce, sai daga baya na ga mutane suna magana a X cewa Facebook da Instagram duk sun samu matsala.”

Nura Haruna Maikarfe ya ce:

"Ni ma na fuskanci wannan matsalar. Wallahi na dauka ko dai data ce ta kare, na duba na ga ina da saura. To da yake an yi mana ruwa, sai na yi tunanin ko tangardar sadarwa daga MTN ne. To dai yanzu nake ganin cewa matsalar daga masu Facebook din ce."

Kara karanta wannan

ESN ta shirya kai hare hare a wasu sassan Najeriya, DSS, sojoji sun dauki mataki

Ana barazanar rufe Facebook a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Meta ya bayyana cewa yana iya rufe Facebook da Instagram a Najeriya saboda tarar makudan kudi da dokoki masu tsauri.

Najeriya ta kakaba wa kamfanin Meta tara da ta kai Dala miliyan 290 bisa zargin karya dokoki daban-daban na kasuwanci da bayanan sirri.

Kamfanin Meta ya kasa kalubalantar wannan hukunci a kotun tarayya, inda aka ba shi wa’adi zuwa karshen Yuni don biyan tarar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com