Iran Ta Sanya Lokacin Jana'izar Ayatollah Ali Khamenei bayan Watanni da Rasuwarsa
- An shirya gudanar da jana'izar tsohon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe yana da shekara 87
- Marigayi Ayatollah Ali Khamenei ya rasa ransa ne sakamakon hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran a watan Afirilun 2026
- An dai shirya gudanar da marigayin ne a watan Yulin 2026 inda za a kwashe kwanaki shida ana jana'iza da makoki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Mahukunta a Iran sun shirya gudanar da jana'izar tsohon jagoran addini na kasar, marigayi Ali Khamenei.
An bayyana cewa za a gudanar jana'izar marigayi tsohon jagoran addinin na Iran ne a cikin watan Yulin shekarar 2026.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa gidajen talabijin na gwamnatin Iran ne suka sanar da hakan a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka mai sukar Najeriya ya jinjina wa Tinubu kan dokar ƴan sandan jihohi
Amurka da Israila sun kashe Ali Khamenei
Amurka da Israila ne dai suka hallaka Ali Khamenei bayan sun kaddamar da hare-hare kan Iran a watan Fabrairun 2026.
Marigayin ya jagoranci kasar Iran na tsawon shekara 37 kafin zuwan lokacin da zai bar duniya, sakamakon kisan da aka yi masa.
Ali Khamenei mai shekara 87 ya karbi jagorancin Iran a shekarar 1989 a hannun Ayatollah Ruhollah Khomenei wanda ya jagoranci juyin juya hali na kasar.
Yaushe za a yi jana'izar Ali Khamenei?
Tun da farko an shirya gudanar da jana’izar Ali Khamenei a watan Maris 2026, amma aka ɗage ta sakamakon yaƙin da aka gwabzawa a wancan lokacin.
A yanzu, za a gudanar da jana’izar ce ta tsawon kwanaki shida, daga ranar 4 zuwa 9 ga Yulin shekarar 2026, jaridar Euronews ta kawo labarin.
Daga cikin abubuwan da za a yi, za a fara da gudanar da jana’izar ƙasa a babban birnin Tehran daga ranar 4 zuwa 6 ga Yulin 2026.
Daga nan za a ci gaba da wasu bukukuwan girmamawa a birnin Qom, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin addini na ƙasar.
Hakazalika, an shirya birne marigayin a ranar 9 ga Yulin 2026 a garinsa na haihuwa wato birnin Mashhad da ke Arewa maso gabashin Iran.
Mojtaba ya gaji Ali Khamenei
Mojtaba Khamenei wanda yake da ne a wajen marigayi Ali Khamenei, ya gaje shi a matsayin Jagoran Koli na Iran a farkon watan Maris, 2026.
Hakan ya sanya ya zama mutum na uku da ya riƙe muƙamin jagoran addini na kasar tun bayan kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1979.
Mojtaba Khamenei, ya kasance ba ya fitowa fili a bainar jama'a tun lokacin da aka fara yaƙin Amurka da Isra'ila a kan kasar Iran.

Source: Getty Images
CIA ta taimaka wajen kashe Ali Khamenei
A wani labarin kuma, kun ji cewa bayanan sirri na hukumar CIA sun taimaka wajen jagorantar hare-haren da Amurka da Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Hare-haren wadanda aka kai a watan Fabrairun 2026, sun yi sanadiyyar hallaka Ayatollah Ali Khamenei da sauran manyan mutane a Iran.
CIA ta gano cewa Ayatollah Ali Khamenei zai halarci wani muhimmin taro da manyan jami’an Iran bayan ta shafe watanni tana bibiyar motsinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

