Manyan Labarai A Yau
Allah ya yi wa daya daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Bauchi rasuwa. Dan majalisar ya yi bankwana da duniya ne a safiyar ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti. Biodun Oyebanji na APC ya samu tazarce a wa'adi na biyu.
Firaministan Italiya, Giorgia Meloni ta mayar da martani mai zafi ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Ta ce ya yi mata karya kan kalaman da ya yi.
Wasu dakarun sojojin Najeriya sun rasa ransu sakamakon fashewar bam a jihar Sokoto. Ana zargin 'yan bindiga ne suka dasa masu bam din a kan hanya.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kebbi tare da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar hallaka wani jagoran 'yan bindiga bayan sun yi artabu a cikin daji.
An tabbatarda rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Arch. Audu Sule Katagum yana dan shekara 69 a duniya, tuni aka fara jimamin wannan rashi.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta kebance wasu mutane da dokar takaita zirga-zirga ba za ta hau kansu ba a zaben cike gurbin dan Majalisar Dawakin Kudu da Warawa.
IPOB ta sanar da dakatar da ofishin shugaba da mukamin Daraktan Radio Biafra da Nnamdi Kanu ke rike da su, tana mai cewa matakin zai kare manufofinta.
A ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti. Akwai matasan 'yan takara a zaben.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari