Babbar Magana: Ministan Tsaron Amurka Ya Aika Sako Mai Zafi ga Shugabannin Iran

Babbar Magana: Ministan Tsaron Amurka Ya Aika Sako Mai Zafi ga Shugabannin Iran

  • Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya gana da manema labarai a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026
  • Pete Hegseth ya aika da sako ga shugabannin Iran yayin da ya bayyana cewa kasar ba ta da sauran karfin soja
  • Ministan tsaron na Amurka, ya bayyana cewa Iran na kokari tono makamanta da aka binne a karkashin kasa sakamakon hare-haren da aka kai

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana kan abin da Iran ke yi yayin tsagaita wuta.

Pete Hegseth ya bayyana cewa a yanzu haka ƙasar Iran tana gudanar da aikin "tono" makamai masu linzami da motocin harba su daga cikin rumbunan da aka yi wa ruwan bam.

Pete Hegseth ya aika sako ga shugabannin Iran
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce Ministan tsaron na Amurka ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Amurka ta aika sako mai zafi, ta kafa sharadin komawa yaki da Iran

Pete Hegseth ya jaddada cewa ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da ikon "sake farfaɗo" da ƙarfin sojinta.

Me Ministan ya gayawa shugabannin Iran?

Hakazalika, ya bayyana cewa Amurka tana kallon duk abin da shugabannin Iran ke yi yayin tsagaita wuta.

Yayin da yake aikara saƙo ga shugabannin Iran, Hegseth ya ce:

“Yayin da kuke gudanar da aikin tono, wanda shi ne ainihin abin da kuke yi, kuna tono makamai daga wuraren da aka lalata da bam, mu kuma ƙara ƙarfi muke yi."
"Kuna tono ragowar injinan harba makamai da makamai masu linzamin ne ba tare da kuna da ikon mayar da wasu a madadinsu ba. Ba ku da masana'antar kera makamai. Ba ku da ikon sake cike gurbin makamanku na kai hari ko na kariya.”

Hotunan tauraron ɗan adam sun nuna manyan injinan haƙa ƙasa suna tono injinan harba makamai masu linzami da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa a daidai lokacin da ake tsagaita wuta.

Batun taimakon makamai daga China

Pete Hegseth ya kuma mayar da martani kan rahotannin da ke cewa China tana shirin aika wa Iran makamai, inda ya ce Amurka ta samu tabbaci cewa hakan ba zai faru ba, tashar CNN ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya yi maganar lokacin kawo karshen yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran

“Shugaba Trump yana da kakkarfar alaƙa kuma ta kai-tsaye da (Shugaban China, Xi Jinping), kuma sun tattauna kan hakan. China ta ba mu tabbacin cewa hakan ba zai faru ba."

- Pete Hegseth

Ministan tsaron Amurka ya ja kunnen shugabannin Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka a wajen kamfe Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

A makon da ya gabata, rahotanni sun ce bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa China tana shirin isar da makaman kariya daga hare-haren sama ga Iran nan da makonni masu zuwa, a cewar wasu mutane uku da ke da masaniya kan bayanan sirrin.

Wannan jawabi na Hegseth na nuni da cewa Amurka tana son nuna wa duniya cewa Iran ta riga ta gurgunce ta fuskar soja, kuma tana amfani da diflomasiyya wajen toshe kowace kofa da Iran za ta iya samun taimako daga waje.

Yunkurin tsige Ministan tsaron Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan majalisar Amurka na jam'iyyar Democrat, sun kaddamar da yunkurin tsige Ministan tsaro, Pete Hegseth.

'Yan majalisar na yunkurin tsige Hegseth ne sakamakon zarge-zarge masu tsanani da suka shafi yadda yake tafiyar da yaƙin Iran da kuma jagorancinsa a ma’aikatar tsaro.

Daga cikin hujjojin da suka gabatar akwai kaddamar da yaƙi kan Iran ba tare da amincewar majalisa ba, wanda hakan ya jefa rayukan sojojin Amurka cikin haɗari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng