Kalaman Atiku Sun Girgiza Fadar Shugaban Kasa, Ta Fadi Abin da Tinubu Zai Yi Masa a 2027

Kalaman Atiku Sun Girgiza Fadar Shugaban Kasa, Ta Fadi Abin da Tinubu Zai Yi Masa a 2027

  • Fadar shugaban kasa ta tanka bayan Alhaji Atiku Abubakar ya yi wasu kalamai kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Hadimin Shugaba Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya bayyana cewa kowa ya san cewa Atiku ne zai zama dan takarar jam'iyyar ADC
  • Daniel Bwala ya bayyana cewa a zaben 2023 lokacin da Atiku yake da gwamnoni bai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya yi wa Atiku Abubakar martani.

Daniel Bwala ya gayawa Atiku Abubakar cewa zai sake shan kaye a hannun jam’iyya mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Hadimin Tinubu ya yi wa Atiku martani
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: @OfficialABAT, @atiku
Source: Facebook

Hadimin na Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya sanar da 'yan Najeriya sabon tsarin da zai kawo idan ya zama shugaban kasa

Atiku Abubakar ya yi maganganu kan 2027

Bwala ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman da Atiku Abubakar ya yi yayin wata hira da aka yi da shi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nemi muƙamin shugabancin ƙasa har sau shida, inda ya bayyana a takardar zaɓe a matsayin ɗan takara sau uku a shekarun 2007, 2019, da kuma 2023.

A yayin shirin, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaɓen 2027 shi ne zai kasance yunƙurinsa na ƙarshe wajen neman shugabancin ƙasar nan.

Haka zalika, Abubakar ya nuna kyakkyawan fata kan gamayyar jam’iyyun adawa da ake ginawa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, inda ya ce duk ɗan takarar da wannan gamayya ta marawa baya zai iya doke Tinubu a 2027.

Martanin Daniel Bwala ga Atiku

A martanin da ya yi, Daniel Bwala, wanda tsohon na-kusa ne da Atiku, ya bayyana jam’iyyar ADC a matsayin taron "shugabannin da suka fusata"

Bwala ya ce kusan tabbas ne Atiku zai kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen, amma Tinubu zai sake doke shi kamar yadda ya yi a 2023, lokacin da tsohon mataimakin shugaban ƙasar yake da gwamnoni da tsarin jihohi a bayansa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta firgita da kalaman Atiku kan 2027, ta yi masa martani

Daniel Bwala ya yi wa Atiku Abubakar martani
Daniel Bwala tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter
“Tsohon maigidana @atiku ya ce ‘tare da ɗan takarar gamayya, Shugaba Tinubu @officialABAT ya riga ya faɗi tun kafin a fara’. Abin dariya (Lol)."
“Amma mun sani cewa kai ne ɗan takarar wannan gamayya. Duk da haka (karka yi fushi yallaɓai), ya doke ka a 2023 lokacin da kake da gwamnoni, jihohi, da goyon baya. Waɗannan gwamnoni da jihohi yanzu suna tare da shi (Tinubu).”
“Tare da gamayyar shugabanni ‘wadanda ba su da tasiri’ kuma suke a fusace, ina shakkun ko Shugaba Tinubu zai ma damu ya duba sakamakon zaɓen a ranar da za a gudanar da shi.”

- Daniel Bwala

Atiku ya fadi shirinsa kan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana gyaran da zai yi idan aka ba shi damar zama shugaban kasar Najeriya.

Atiku Abubakar wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa zai yi fafutukar ganin an yi wa tsarin mulki gyara.

Kara karanta wannan

Atiku: "Yadda ADC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027"

Hakazalika, Atiku ya ce za a yi gyaran ne domin tabbatar da tsarin karɓa-karɓar kujerar shugaban ƙasa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng