2027: Atiku Ya Sanar da 'Yan Najeriya Sabon Tsarin da Zai Kawo Idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana sabon abin da yake son kawowa a Najeriya idan aka ba shi damar shugabanci
- Atiku ya bayyana cewa zai kawo gyara kan yadda ake takarar shugabancin kasar nan idan aka ba shi dama
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa zai yi wannan gyaran ko da kuwa shi ne kadai abin da zai yi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai yi fafutukar ganin an yi wa tsarin mulki gyara.
Atiku ya ce za a yi gyaran domin tabbatar da tsarin karɓa-karɓar kujerar shugaban ƙasa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Source: Facebook
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Prime Time na tashar Arise News a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027
Wane tsari Atiku Abubakar zai kawo?
Atiku Abubakar ya ce yana goyon bayan tsarin karba-karba, yana mai nuni da cewa sanya hakan a cikin tsarin mulki zai samar da ingantaccen tsarin raba mulki cikin adalci da kwanciyar hankali.
“Idan ni ne shugaban ƙasa, koda kuwa wannan ne kaɗai gyaran da zan iya yi, zan yi ƙoƙari wajen ganin an tabbatar da hakan."
- Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce jam’iyyar PDP ita ce kaɗai jam’iyyar siyasa da ke da tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkinta.
“Jam’iyyar siyasa ɗaya tilo da take da batun karba-karba a tsarin mulkinta ita ce PDP. Sauran ba su da shi. Idan ma akwai wani abu, sauran jam’iyyun rance suke yi ko kuma koya suke yi daga wurin PDP."
- Atiku Abubakar
Ya kuma yi magana kan raba ragamar shugabanci tsakanin Arewa da Kudu, inda ya lura cewa Kudu ta riƙe ofishin shugaban ƙasa na tsawon lokaci fiye da Arewa.
“Kudu ta yi mulki na tsawon shekaru 18, Arewa kuma shekaru 10; don haka ina aka bari a baya?”
- Atiku Abubakar
Nadamar Atiku kan shawarar Alex Ekwueme
Atiku ya tuna yadda ya nuna amincewarsa ga wata shawara ta mayar da shugabanci ya zama na karɓa-karɓa wadda marigayi tsohon mataimakin shugaban kasa Alex Ekwueme ya bayar lokacin muhawarar tsarin mulki a baya.
“Akwai muhawara tsakanina da marigayi Alex Ekwueme. Ya ba da shawarar a sanya batun karɓa-karɓar shugabancin ƙasa a cikin tsarin mulki, ni kuma na nuna rashin amincewa ta."
“Saboda muna da iko da kusan kashi 60 zuwa 70 na wakilai, gyaran bai samu nasara ba.”
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Sai dai Atiku ya ce daga baya ya yi da-na-sani kan wancan mataki nasa.
“Yanzu idan na duba baya, lokacin da na halarci jana’izarsa, na amince cewa na yi kuskure. Ya kamata na goyi bayan wannan gyara, da yanzu shugabancin ƙasa yana zagayawa dukkan shiyyoyin ƙasar nan."
- Atiku Abubakar
Atiku ya magantu kan farin jininsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana farin jinin da yake da shi a Arewa.
Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana da karfin goyon bayan siyasa a Arewacin Najeriya fiye da sauran fitattun ‘yan siyasa daga yankin.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa daga cikin waɗanda ya ke ganin ya fi yawan masoya akwai Sanata Rabiu Musa da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

