Shin da Gaske Pantami Ya Fara Yawo da 'Yan Dabar Siyasa? An Gano Gaskiya
- Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami na daga cikin mutanen da suka nuna sha'awar neman kujerar gwamnan Gombe
- An yada wani bidiyo da ke ikirarin cewa an ga Farfesa Pantami tare da 'yan daba yayin wata ziyara da ya kai jihar Gombe
- An sanya rariya an tankade bidiyon, inda aka gano gaskiya ko rashin gaskiyar ikirarin da aka yi a kan tsohon Ministan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - An yada wani bidiyo da ke ikirarin cewa an ga Farfesa Isa Ali Pantami tare da 'yan daba.
An dai yi ikirarin cewa an ga tsohon Ministan na sadarwa tare da wasu ‘yan daba ɗauke da makamai a wani taron siyasa a jihar Gombe.

Source: Twitter
Wani shafi a dandalin X mai suna ADC Vanguard (@ADCvanguard), ya wallafa wani bidiyo yana iƙirarin cewa an ga tsohon Ministan da 'yan daba.
An yi ikirarin ganin Pantami da 'yan daba
An wallafa saƙon ne da misalin ƙarfe 8:19 na dare a ranar 15 ga Afrilu, 2026.
Ya zuwa lokacin gudanar da wannan binciken, saƙon ya samu kallon mutane 79,200, alamar so 479, sake yada shi sau 108, da kuma sharhi guda 63.
Sakon na cewa:
“Labari mai ɗumi-ɗumi: An hango Sheikh Pantami tare da ‘yan daba ɗauke da manyan makamai a kan hanyarsa ta zuwa taron siyasa. Kwadayinsa na son zama gwamnan jihar Gombe yana ƙara zama abin takaici."
Ganin muhimmancin wannan zargi, jaridar Daily Trust ta gudanar da binciken gaskiya.
Me bincike ya nuna?
Mutumin da aka gani a tsakiyar bidiyon lallai tsohon Ministan na sadarwa ne watau Farfesa Isa Ali Pantami.
Bincike ya nuna cewa bidiyon ya ɗauki lokacin da ya isa jihar Gombe ne a ranar 10 ga Afrilu, 2026, inda taron jama'a suka tarbe shi a filin jirgin sama da sauran sassan jihar, ciki har da ƙaramar hukumar Billiri.
Wannan ziyara tana ɗaya daga cikin jerin tarurrukan da ya halarta a mahaifarsa.
Binciken hotunan bidiyon ta hanyar amfani da manhajar InVID da binciken hotuna ya kai ga wani bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok na Pantami, wanda ya nuna irin wannan yanayi.
Bidiyon ya nuna dimbin jama'a suna yi masa maraba a Billiri yayin da yake tare da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a wata ziyarar aiki.
Binciken daki-daki na kowane sashe na bidiyon ya nuna jami'an tsaro sanye da baƙaƙen kaya da gilasai, waɗanda wasu daga cikinsu ke ɗauke makamai kamar yadda ƙa'idar aikin jami'an tsaro take.
Bidiyon ya kuma nuna matasa ɗauke da gora, sai dai waɗannan gorori ne na katako na yau da kullum, ba wasu manyan makamai masu kisa ba.

Source: Facebook
Babu gaskiya a cikin ikirarin
Babu wata shaida a cikin bidiyon da ke goyon bayan iƙirarin cewa mutanen da ke tare da Pantami “’yan daba” ne ɗauke da manyan makamai.
Iƙirarin cewa an ga Pantami tare da ‘yan daba ɗauke da manyan makamai ba shi da tushe ballantana hujja.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta kinkimo wa mutane aiki, bashin N724,000 ya hau kan kowane 'dan Najeriya
Bayan jami’an tsaro ɗauke da bindigogin aiki, babu wani mutum a cikin bidiyon da aka gani tare da haramtattun makamai ko manyan makamai.
Pantami ya karyata karyar da aka yi masa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi martani kan ikirarin cewa Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bukaci ya hakura da takara a zaben 2027.
Rahoton da aka yada ya nuna cewa gwamnan ya bukaci tsohon Ministan sadarwar a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari da ya goyi bayan dan takarar da jam'iyyar APC ta amince da shi.
Farfesa Pantami ya fito ya ƙaryata wannan labari gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa.
Asali: Legit.ng

