Shugaban Amurka Ya Kira Sarkin Qatar Ta Wayar Tarho, An Ji Maganar da Suka Yi kan Iran
- Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi magana da Shugaba Donald Trump ta wayar salula kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya
- Fadar Sarkin Qatar ta tabbatar da tattaunawar shugabannin kasashen biyu, inda ta jero muhimman batutuwan da suka tabo
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sake shirya tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a karo na biyu a birnin Islamabad
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Qatar - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kira Sarkin kasar Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ta wayar tarho a yau Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026.
Bayanai sun nuna cewa shigabannin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa musamman yakin Amurka/Isra'ila da Iran, wanda ya shafi Qatar da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Trump ya kira Sarkin Qatar ta wayar tarho
Tashar Al-Jazeera News ta ruwaito cewa Fadar Sarkin Qatar (Amiri Diwan) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba.
Ta bayyana cewa Sheikh Al Thani da Shugaba Trump sun yi duba tare da tattaunawa kan sababbin abubuwan da ke faruwa a yankin da ma duniya baki ɗaya sakamakon yakin Iran.
Sanarwar ta ce daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna akwai tsaron hanyoyin ruwa na duniya, daidaiton kasuwannin makamashi, in ji tashar NBC News.
Abin da Sarkin Qatar ya tattauna da Trump
Haka zalika Trump da Sarkin na Watar sun duba hanyoyin samar da kayayyaki a duniya, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar takaddama kan toshe mashigar ruwa ta Hormuz.
Sarkin na Qatar ya jaddada muhimmancin hadin kao da dagiya domin dakile ƙarin tashin hankali a yankin, yana mai kira ga haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin Amurka da Iran.
Kalaman da Sarkin ya fitar ya fadawa Trump
A yayin tattaunawar, Sarkin Qatar ya jaddada muhimmancin ƙara haɗin gwiwar ƙasashen duniya domin dakile ƙarin tashin hankali da kuma hana rikicin faɗaɗa zuwa wasu yankuna.
Ya nuna cewa wajibi ne ƙasashe su haɗa kai wajen nemo mafita ta hanyar diflomasiyya maimakon amfani da ƙarfin soja, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Source: Getty Images
Saboda haka, ana ganin irin waɗannan tattaunawa tsakanin manyan shugabanni kamar na Qatar da Amurka na da matuƙar muhimmanci wajen rage zafin rikicin da kuma samar da mafita mai ɗorewa.
Ana fatan irin wannan hulɗa za ta taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a yankin da ke da matuƙar tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Iran ta mika sakon godiya ga kasar Pakisan
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta godewa Pakistan bisa rawar da take takawa wajen ganin an yi sasanci tsakaninta da Amurka domin samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya mika wannan sakon godiya jim kadan bayan ya karbi tawagar Pakistan a filin jirgin sama na birnin Tehran.
Ya jaddada cewa haɗin gwiwar Iran da Pakistan wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na nan daram kuma suna tafiya tare.
Asali: Legit.ng

