"Ina Girmama Ka"; Tsohon Minista ya Dura kan Sheikh Jingir kan Tallata Muslim Muslim

"Ina Girmama Ka"; Tsohon Minista ya Dura kan Sheikh Jingir kan Tallata Muslim Muslim

  • Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi magana kan zabar Muslim-Muslim a 2027
  • Sheikh Jingir ya bukaci musulmai su fito su gyara kuri'unsu domin nunawa duniya cewa sun fi yawa a Najeriya
  • Kalaman na Sheikh Jingir sun jawo martani daga wajen jakadan Najeriya a kasar South Africa, Femi Fani Kayode

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jakadan Najeriya a kasar South Africa, Femi Fani Kayode, ya yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir martani kan goyon bayan muslim-muslim.

Femi Fani Kayode ya yi martanin ne bayan Sheikh Jingir ya kira ga musulmi su sake goyon bayan tikitin muslim-muslim a zaben 2027.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi martani ga Sheikh Jingir
Femi Fani Kayode da Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Femi Fani-Kayode
Source: Facebook

Femi Fani Kayode ya yi martanin ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya shiga damuwa bayan tura kudi masu yawa a asusunsa

Me Sheikh Jingir ya fada kan muslim-muslim?

A cikin wani bidiyo da Datti Assalafy ya sanya a Facebook, Sheikh Jingir ya bukaci jama'a su sake goyon bayan tikitin muslim-muslim.

"In daga tutar musulunci in kira jama'a ku taho mu yi muslim-muslim. Na sani cewa kafirai na jin zafin wannan kalma, to amma ba akwai kiristoci ba, ba akwai yahudawa ba, ba akwai masu bautar magiro ba, ni musulmi mai wa'azin musulunci da na ce muslim-muslim me na taba na su."
"Na hana kirista-kirista ya fada ne, na hana bagiro-bagiro ya fada ne, na hana dan tantal batete ya fada ne, amma ni a matsayin musulmi, muslim-muslim."
"Amma ai wani zai ce aa ai dimokuradiyya ne, ai akwai su wane ba sa sallah, kai ne wakilinsu? Mu kuma muna sallah muna azumi, kuma dimokuradiyya kun ce masu yawa su ne ke rinjaye. Jamaa gwauro da gwauruwa Allah ya ba ku aboka zaman tare na aure."

Kara karanta wannan

Izala ta shirya babban taro na tarihi a Abuja, an gayyaci manyan baki

"Ina kira a gare ku dan Allah kowa ya je ya gyara kuri'a, ku nunawa duniya cewa karya kafirai suke yi da suka ce sun fi mu yawa a Najeriya. Ba don Allah ya taimake mu na ce muslim-muslim ba, da mai rabon jini sai ya yi tunanin sun fi mu yawa."
"Da aka buga, Allah ya taimake mu muka kwantara su da kasa, su zo na biyu ma ba su zo ba. Ko sun zo? Sai na uku bayan murdiyarsu duka. Don haka kuri'ata ta musulunci ce. Jama'ar musulmi ta ku fa."

- Sheikh Sani Yahaya Jingir

Wane martani Femi Fani Kayode ya yi?

Femi Fani Kayode ya bayyana cewa kalaman da Sheikh Jingir ya yi, na tsatstsauran ra'ayi ne, kuma ba su da ce ba a kasa irin Najeriya.

"Ina matuƙar girmama Sheikh Jingir, amma dole ne in bayyana cewa kalaman tsattsauran ra’ayin da ya yi amfani da su a nan ba su taimaka mana ba, kuma ba su dace da gaskiya ba."
"Abin da ya fi muni shi ne yadda kalaman suke da matuƙar tayar da hankali. Ya kamata a lura cewa wannan hanya ce mai matuƙar hatsari, kuma abu ne mai sauƙin jefa al’umma cikin matsala, don haka ya fi kyau a guje mata."

Kara karanta wannan

VeryDarkMan: Dan Tiktok ya gindaya sharuddan amsa gayyatar 'yan sanda

"Najeriya ba ƙasar Musulmi ba ce, haka kuma ba ƙasar Kirista ba ce. Ƙasa ce mai bin tsarin mulkin zamani kuma mai addinai daban-daban, wadda ta ƙunshi Musulmai da Kiristoci kusan daidai gwargwado. Wannan ne ƙarfimmu."
"Muna goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027, kamar yadda muka yi a 2023, ne kawai saboda ƙwarewa, iyawa, gaskiyar manufa, ɗabi’a, amfanin shugabanci da kuma ƙarfin samun kuri’u na ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa, da kuma yadda suke da ikon sauke nauyin da ke kansu, ba don su Musulmai ba ne."
"Wata rana ma za mu iya samun tikitin Kirista da Kirista, domin komai yana yiwuwa da ikon Allah. Mu bar addini a wajen siyasa, mu mayar da hankali kan batutuwa, manufofi da kuma halayen ‘yan siyasa."
"Al’ummar Kirista ta samu kyakkyawan matsayi a Najeriya cikin shekaru ukun da suka gabata a ƙarƙashin wannan gwamnati, har ma fiye da yadda ta samu tsakanin 2015 zuwa 2023, duk da cewa a wancan lokacin muna da tikitin Musulmi da Kirista."
"Bai kamata mu bari wannan batu ya raba kanmu ba. Mu ‘yan Najeriya ne kafin mu zama Kiristoci ko Musulmai, kuma dole ne ba kawai mu tsaya a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya ba, har ma mu je rumfunan zaɓe a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka tsunduma cikin talauci

"Mun shawo kan rashin jituwa da ya taso kan addini a 2023 kuma muka lashe zaɓen shugaban ƙasa, kuma da yardar Allah za mu sake yin hakan a 2027."

- Femi Fani Kayode

Femi Fani Kayode ya soki kalaman Sheikh Jingir
Femi Fani Kayode na karanta wata takarda Hoto: Femi Fani-Kayode
Source: Facebook

Sheikh Jingir ya soki nadin Amupitan

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya soki nadin shugaban INEC.

Malamin ya bayyana naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin babbar barazana ga ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng