Ana Shirin Sake Zama, Trump Ya Fadi Abin da Zai 'Harzuka' Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Ana Shirin Sake Zama, Trump Ya Fadi Abin da Zai 'Harzuka' Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya dauko batun toshe tashoshin jiragen ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Trump ya yaba da matakin Amurka na killace tashoshin jiragen ruwan, inda ya ce hakan ya hana Iran gudanar da harkokin kasuwanci
  • Shugaban Donald Trump ya kuma yi maganar yiwuwar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaba Donald Trump ya jinjinawa matakin da Amurka ta ɗauka na killace tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Trump ya bayyana matakin a matsayin "abin mamaki" kuma ya tabbatar da cewa ya dakatar da kusan dukkan harkokin tattalin arziƙin ƙasar.

Trump ya yaba da abin da Amurka ta yi wa Iran
Shugaba Donald Trump a fadar White House Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Tashar CNN ta ce Trump ya bayyana hakan ne ayin da yake magana da manema labarai a fadar White House kafin ya nufi birnin Las Vegas,a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaron Amurka ya aika sako mai zafi ga shugabannin Iran

Me Donald Trump ya ce kan Iran?

“Muna samun nasara sosai game da hakan, dangane da daukacin halin da ake ciki a Iran. Wannan killace hanyoyin ruwa abin mamaki ne. Yana aiki sosai cikin ƙarfi da karsashi. Kuma ina jin muna samun ci gaba sosai a kan hakan."

- Donald Trump

Shugaban na Amurka ya yi iƙirarin cewa wannan yunƙuri ya sa Iran ta gaza gudanar da kowane irin kasuwanci, yana mai nuni da abin da ya kira rugujewar ƙarfin sojinta baki ɗaya.

“Abin ya tabbata, kuma ba sa yin wani kasuwanci. Ba su da ikon yin kowane irin kasuwanci saboda wannan killace su da aka yi."
"Don haka, rashin rundunar sojan ruwa, rashin rundunar sojan sama, rashin makaman kariya daga hare-haren sama; ba su da komai, komai ya ƙare.”

- Donald Trump

Kasar Amurka ta tsanantawa Iran

Wannan furuci na shugaban ya zo ne a daidai lokacin da manyan jami’an sojin Amurka ke nuna alamun shirye-shiryen tsananta matakan killace kasar.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Amurka ta aika sako mai zafi, ta kafa sharadin komawa yaki da Iran

Trump ya ƙara da cewa:

"Babu wani jirgin ruwa da zai iya wuce rundunar sojan ruwanmu.”
Trump ya yi maganar tsawaita yarjejeniyar Amurka da Irsn
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Me Trump ya ce kan tsawaita yarjejeniya?

Tashar CBS ta ce Shugaba Trump ya ce yana iya yiwuwa ba zai buƙaci tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ba, wadda za ta ƙare a mako mai zuwa, koda yake ya yi barazanar komawa yaƙi idan ɓangarorin biyu ba su cimma yarjejeniya ba.

“Zan iya gaya muku cewa abubuwa suna tafiya da kyau. Ban tabbata ko akwai buƙatar tsawaita yarjejeniyar ba.”

- Donald Trump

Ya ƙara da cewa Iran tana ɗokin cimma yarjejeniya, kuma ta nuna cewa "tana shirye ta aikata abubuwan da ba ta shirya aikatawa ba watanni biyu da suka gabata."

Trump ya sanar da tsagaita wuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da tsagaita wuta tsakanin Israila da Lebanon.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa kasashen biyu sun amince da jarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 10.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa tsagaita wutar ta biyo bayan tattaunawa ta musamman da ya yi da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma Shugaban Lebanon Joseph Aoun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng