Gwamnatin Tinubu Na Shirin Sake Karbo Bashi daga IMF? Minista Ya Yi Bayani
- Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi tayin ba da bashi ga kasashen Afrika da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya shafa
- Ministan kudi na Najeriya, Wale Edun, ya koka da cewa mafi yawan kasashen Afrika na fuskantar matsalar fadawa cikin mawuyacin hali kan bashi
- Wale Edun ya kuma bayyana matsayar Najeriya kan ko a halin yanzu tana da shirin tunkarar IMF domin sake neman bashi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Ministan kudi, Wale Edun, ya yi magana kan batun sake tunkarar asusun ba da lamuni na duniya (IMF) don neman bashi.
Wale Edun ya bayyana cewa babu wani shiri na tunkarar asusun IMF domin neman bashi.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026 yayin taron manema labarai na ministoci a taron bazara na IMF da Bankin Duniya da ke gudana a Washington DC.

Kara karanta wannan
Ana shirin sake zama, Trump ya fadi abin da zai harzuka Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Bashin Najeriya ya karu
Jawabin Edun ya zo ne kwana guda bayan da Ofishin Kula da basussukan na kasa (DMO) ya bayar da rahoton cewa jimillar bashin da ake bin gwamnatin tarayya da na jihohi ya ƙaru da Naira triliyan 14.
Hakan ya sa bashin ya kai Naira triliyan 159.27 a watanni uku na karshen shekarar 2025.
A ranar 31 ga Maris, majalisar dokokin ƙasa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓar bashin ƙasashen waje na Dala biliyan 6, matakin da ya haifar da damuwa game da yadda Najeriya ke amfana da ribar hauhawar farashin mai.
Hukumar IMF ta bayyana cewa tana sa ran aƙalla ƙasashe 12 za su nemi tallafin kuɗi tsakanin Dala biliyan 20 zuwa Dala biliyan 50 nan ba da jimawa ba.
Hakazalika, hukumar ta kuma buƙaci ƙasashen Afirka da rikicin Gabas Ta Tsakiya ya shafa da kada su yi jinkirin neman tallafin kuɗi idan buƙatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta kinkimo wa mutane aiki, bashin N724,000 ya hau kan kowane 'dan Najeriya
Shin Najeriya za ta karbo bashi daga IMF?
Da yake magana kan wannan tayin, Edun ya ce Najeriya ba ta da irin wannan shiri, jaridar The Punch ta fitar da labarin a yau.
“Najeriya ba ta da shiri a halin yanzu na tunkarar IMF ko wani wurin neman bashi na daban."
- Wale Edun

Source: Twitter
Edun ya hango matsala ga kasashen Afrika
Yayin da yake tsokaci baki ɗaya kan yanayin kasafin kuɗi a yankin Afirka, Edun ya ce ƙasashe da dama a nahiyar suna kusa da fadawa cikin mawuyacin halin bashi.
“Dangane da adadin bashi, kusan rabin ƙasashen Afirka suna cikin matakin fuskantar barazanar bashi, ko ma matakin kunci."
- Wale Edun
Ministan ya ce hakan na faruwa ne sakamakon tsadar kudin ruwan bashi da ƙasashen Afirka ke biya.
Bashin da ya hau kan 'yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jimillar bashin da gwamnatin tarayya ta kinkimo ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan
Yakin Iran, Amurka: Najeriya da wasu kasashe na iya samun tallafin dala biliyan 50
A cewar wani bincike hakan na nufin idan aka raba wadannan kudade kan 'yan Najeriya, kowane mutum daya ana bin shi bashin kusan N724,000.
Bashin ya ƙaru daga Naira tiriliyan 153.29 a watan Satumba 2025 zuwa Naira tiriliyan 159.28 a watan Disamba 2025.
Asali: Legit.ng