Shugaba Trump Ya Yi Maganar Lokacin Kawo Karshen Yaki da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Shugaba Trump Ya Yi Maganar Lokacin Kawo Karshen Yaki da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake tabo batun lokacin kawo karshen yakin da kasarsa ke yi da Iran
  • Donald Trump ya bayyana cewa za a iya kawo karshen yakin ta hanyar cimma yarjejeniya ko akasin haka
  • Shugaban na Amurka ya kuma nuna cewa nan da kwanaki biyu masu zuwa wani abin ban mamaki zai iya faruwa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin magana kan yakin da kasarsa ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Donald Trump ya bayyana cewa yaƙi da ƙasar Iran na iya ƙarewa nan kusa, inda ya shaida wa duniya cewa su zuba ido su ga "wasu kwanaki biyu masu ban mamaki".

Trump ya ce za a kawo karshen yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Dan jaridar ABC News Jonathan Karl ya ce Trump ya sanar da shi hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana mai jan hankali, da alamu Amurka da Iran za su koma Islamabad

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Amurka da ke gudanar da toshe hanyoyin ruwa, suka tilastawa jiragen ruwan Iran komawa baya yayin da suke ƙoƙarin barin tashoshin kasar.

Trump a kan kawo karshen yaki da Iran?

Shugaba Trump ya bayyana cewa ba ya tunanin akwai bukatar sake tsawaita yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran.

"Ina jin za ku ga wasu kwanaki biyu masu ban mamaki a gaba. Da gaske nake."

- Donald Trump

Da aka tambaye shi ko yaƙin zai ƙare ne da wata yarjejeniya ko akasin hakan, sai ya kada baki ya ce:

"Zai iya ƙarewa ta kowane ɓangare, amma ina jin yarjejeniya ta fi dacewa domin hakan zai ba su damar sake gina abubuwan da aka lalata."
"Haƙiƙa yanzu suna da gwamnati ta daban. Ko ma dai yaya abin yake, mun riga mun kawar da masu tsattsauran ra'ayi. Sun tafi, ba sa tare da mu yanzu."
"Idan ba ni ne shugaban ƙasa ba, da duniya ta shiga babbar matsala."

- Donald Trump

Trump ya ce nan ba da jimawa za a kawo karshen yako da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na jawabi Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Shirin sabuwar tattaunawa a Islamabad

Jami’ai daga Pakistan, Iran, da wasu ƙasashen yankin Fasha sun tabbatar da cewa tawagogin tattaunawa na Amurka da Iran na iya komawa Islamabad a ƙarshen wannan mako.

Kara karanta wannan

Duk da tsagaita wuta, Trump ya sake yin babbar barazana ga Iran

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa akwai yiwuwar tawagar Pakistan za ta isa Iran a ranar Laraba domin isar da saƙonni daga Washington.

Tattaunawar ƙarshen makon da ya gabata ta ruguje ne ba tare da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da Trump ya ƙaddamar tare da Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 ba.

Shugaban Iran ya magantu kan yaki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasarsa ba ta da niyyar mika wuya.

Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa babu wata babbar kasa a duniya da za ta iya tursasa al’ummar Iran yin biyayya ko mika wuya.

Shugaban na Iran ya nuna cewa babu dalilin da zai sanya a kai hare-hare kan kasarsa domin hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng