Gwamnatin Tinubu na Samun N6,240 a kowane Buhun Siminti a Najeriya? Gaskiya Ta Fito

Gwamnatin Tinubu na Samun N6,240 a kowane Buhun Siminti a Najeriya? Gaskiya Ta Fito

  • Jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na samun N6,240 daga kowane buhun siminti a Najeriya ba gaskiya ba ne
  • A yan kwanakin nan, wani rahoto da mutane ke yadawa ya yi ikirarin cewa gwamnati na karbar N6,240 a farashin kowane buhun siminti
  • Sai dai kamfanin Dangote Group ya fito karara ya musanta wannan labari, yana mai bayyana shi a matsayin karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - A 'yan kwanakin nan, wata jita-jita ta yi yawo a kafafen sada zumunta kan kudin gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu kan kowane buhun siminta.

Jita-jitar wacce ba ta da wata madogara mai karfi, ta yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu na karbar fiye da N6,000 daga kowane buhun siminti da aka sayar a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwammati ta kinkimo wa mutane aiki, bashin N724,000 ya hau kan kowane 'dan Najeriya

Dangote.
Wurin kasuwancin buhunan simintin Dangote a Najeriya Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Shafin Extra News Blog ya wallafa wannan labari a Facebook, inda ya yi ikirarin cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ne ya fada da bakinsa.

Yadda jita-jitar ta yi yawo a Najeriya

Jita-jitar ta yi ikirarin cewa:

“Gwamnatin Tinubu na karɓar kwabo 52 a duk N1 ta siminti. Wato N6,240 daga kowane buhu na siminti. Duk da haka har yanzu suna ci gaba da aro kudi, me suke yi da kuɗin?”

Wannan kalamai sun haifar da martani daban-daban a tsakanin 'yan Najeriya, musamman ganin yadda kasar ke ci gaba da dogara da bashi duk da dimbin harajin da take samu daga manyan masana'antu.

Yawancin 'yan kasa sun nuna shakku kan yadda ake sarrafa irin wadannan kudaden shiga a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki, tashin farashin kayan gini, da kuma matsalolin ababen more rayuwa.

Mene ne gaskiyar wannan labari?

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

Kamfanin Dangote Group ya musanta wata jita-jitar da ke yawo a shafukan sada zumunta, wadda ake zargin cewa gwamnatin Tinubu na samun kuɗi har N6,200 daga kowanne buhun siminti da ake sayar wa a Najeriya.

Kamfanin Dangote ya mayar da martani ne a ranar Laraba ta hanyar wallafa hoton jita-jitar da ake yadawa a shafinsa na X, inda ya bayyana ta da kalmar “ƙarya” ba tare da ƙarin bayani ba.

Aliko Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote Hoto: @Dangotegroup
Source: Getty Images

Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da yaɗuwar bayanan ƙarya a kafafen sada zumunta, musamman amfani da fasahar zamani wajen ƙirƙirar bidiyo da hotuna na bogi domin yaɗa manufofin siyasa.

Dangote ya shige jerin mutane mafi tasiri

A wani labarin, kun ji cewa an fitar da jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya a shekarar 2026, kuma hamshakin dan kasuwa a Najeriya, Aliko Dangote ya shiga cikinsu.

Dangote, wanda aka saka a rukunin “Titans”, shi ne dan Najeriya daya tilo a jerin na 2026, duk da cewa ba shi kadai ba ne daga Afirka.

Wannan shi ne karo na biyu da Dangote ke shiga jerin mutane 100 mafi tasiri da ake fitarwa, bayan an taba karrama shi a 2014 saboda tasirinsa a kasuwanci da ayyukan jin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262