Lamari Ya Girma: Za a Sake Kai Korafi gaban Trump kan Kashe Kashe a Arewa
- Kungiyar Idoma a Amurka ta yanke shawarar kai ƙorafi ga Shugaba Donald Trump kan kashe-kashe da matsalar tsaro
- Kungiyar ta ce za ta nemi ƙarin kulawar ƙasa da ƙasa da tallafin jin ƙai da diflomasiyya ga al’ummomin Benue Ta Kudu
- Haka kuma, kungiyar ta shirya kai aikin lafiya Najeriya a Disamba 2026, tare da ba da magunguna da shawarwarin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kungiyar Idoma da ke ƙasashen waje za ta kai ƙorafi ga Shugaba Donald Trump kan kashe-kashen Benue
Kungiyar da ke Amurka ta yanke shawarar kai ƙorafi ga Trump kan kashe-kashe, ƙaurar da jama'a da tabarbarewar tsaro a Benue ta Kudu da sauran sassan jihar.

Source: Getty Images
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan kammala taronta na shekara karo na 30 da aka gudanar a Virginia, Amurka, cewar Tribune.
Yan Najeriya za su kai korafi ga Tinubu
Taron ya haɗa wakilai, sarakunan gargajiya, wakilan gwamnati da mambobin Idoma da ke ƙasashen waje.
Mahalarta sun nuna matuƙar damuwa kan rashin tsaro, kashe-kashe da ƙaurar da fararen hula ke fuskanta a Benue South da sauran al’ummomin jihar.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatin Benue da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa da ɗorewa domin kare rayuka da dawo da zaman lafiya a wuraren da matsalar ta shafa.
Ta ce bai kamata a bar ci gaba da asarar rayuka ya zama abin da aka saba gani ba, tana mai jaddada buƙatar gaggauta magance matsalolin tsaro da na jin ƙai da al’ummar ke fuskanta.
A cewar sanarwar, taron ya amince da gabatar da ƙorafi ga Donald Trump domin jawo hankalin duniya kan kashe-kashe, ƙaurar da jama'a da matsalar jin ƙai da ke faruwa a Benue ta Kudu.
Kungiyar ta ce ƙorafin zai nemi ƙarin kulawar ƙasa da ƙasa da kuma samun tallafin jin ƙai da na diflomasiyya ga al’ummomin da matsalar rashin tsaro ta shafa.
Haka kuma, kungiyar ta yanke shawarar yin ƙoƙari domin samun damar da Och’Idoma V, Mai Martaba Agaba’Idu John Elaigwu Odogbo Obagaji, zai gabatar da matsalolin tsaro da jin ƙai na mutanen Idoma ga wasu mambobi da kwamitocin Majalisar Dokokin Amurka.

Source: Original
Kungiya ta fadi muhimmancin shugabanci
Kungiyar ta ce wannan shiri zai ƙara wa fafutukarta ƙarfi, tana mai cewa muryar ‘yan Idoma da ke ƙasashen waje dole ta kasance tare da taimakon zahiri ga mutanen da ke gida.
Dangane da shugabanci da zaɓe, taron ya sake jaddada muhimmancin gaskiya a shugabanci da aikin gwamnati, tare da kira ga shugabanni na yanzu da masu son shugabanci su kasance masu rikon amana, gaskiya da sadaukar da kai.
Kungiyar ta kuma amince da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan masu zaɓe da ilimantar da jama’a kan harkokin ɗan ƙasa gabanin zaɓukan da ke tafe.
IAUSA ta yi kira ga masu zaɓe a Benue South da su tantance ‘yan takara bisa gaskiya, ƙwarewa, rikon amana, hangen nesa da halayensu, maimakon kabilanci, jam’iyya ko karɓar kuɗi, cewar Punch.
Muslim/Muslim: An kai korafi ga Trump
An ji cewa wasu kungiyoyin Kirista da masu rajin kare hakki daga jihohi 36 da Abuja sun aika wa Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka takarda.
Kungiyoyin sun ce ci gaba da tsayawa da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2027 na iya kara tabarbarewar tsaron Kiristoci.
Kungiyar Christian Youth Alliance of Nigeria (CYAN) ta ce lakabin Country of Particular Concern (CPC) bai dakatar da kashe-kashen Kiristoci ba.
Asali: Legit.ng


