Iran Ta Gindaya Sharudda ga Amurka kan Bude Hormuz, Ta Tabo Batun Sanya Haraji
- Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya bayyana abin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da Amurka kan mashigar Hormuz
- JD Vance ya ce Washington na sa ran fitar da man fetur da iskar gas daga kasashen Gulf za ta koma yadda take kafin yakin
- Babban jami’in tsaron Iran ya ce Amurka dole ta sauya dabi’arta kafin a sake bude mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Mataimakin Shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya bayyana maganar da Iran ta sanar da Amurka kan mashigar ruwa ta Hormuz.
Vance ya bayyana cewa Iran ta sanar da Amurka cewa ba ta da wani shiri na kakaba kudin harajin wucewa kan jiragen ruwa da ke ratsa mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Aljazeera ta kawo rahoton cewa JD Vance ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Fox News ta kasar Amurka.
Me Iran ta gayawa Amurka?
Mataimakin shugaban kasar na Amurka ya ce wasu mutane a cikin gwamnatin Iran suna magana kan yiwuwar kakaba irin wannan kudin.
“Ka ga, wasu mutane a cikin gwamnatin Iran, ba shakka, suna magana kan kakaba kudin harajin wucewa. Amma Iran ta sanar da mu cewa ba ta da wani shirin kakaba kudin wucewa kan mashigar Hormuz,” in ji Vance.
Ya kuma ce Washington na sa ran fitar da man fetur da iskar gas daga kasashen Gulf za ta koma matakin da take kai kafin yakin.
“Wannan shi ne abin da Iran ta sanar da mu cewa za ta yi. Haka kuma shi ne abin da daukacin hadakar kasashen Gulf ke son yi. Amma, ka sani, ba ma yarda da magana kawai; muna tabbatarwa. A zahiri, ba mu kallon kalaman mutane, muna kallon ayyukansu,” in ji shi.
Iran ta fadi sharuddan bude Hormuz
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Mohammad Bagher Zolghadr, shi ne sabon jami’in Iran da ya yi magana kan “sharuddan” da kasar ta gindaya domin sake bude mashigar Hormuz.
A cikin wata sanarwa da gidan rediyon IRIB na Iran ya wallafa, Zolghadr ya ce dole Amurka ta “gyara dabi’arta”, inda ya gabatar da bukatun Iran kamar haka:
- Ta kawo karshen barazanar da take yi wa Iran da “abubuwan da take ganin suna da tsarki”
- Ta dakatar da ayyukan soji na dindindin a kan Iran da kawayenta na yankin
- Ta janye jiragen ruwan yaki da na sama na Amurka da ke da hannu wajen killace Iran
- Ta biya Iran diyya kan barnar da aka yi mata a lokacin rikicin baya-bayan nan
- Ta dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran
- Ta saki kadarorin Iran da aka kwace

Source: Twitter
Zolghadr ya ce:
“Majalisar Tsaron Kasa ta Koli ba za ta ja da baya daga wadannan bukatu ba, ko a lokacin yaki ko kuma a tattaunawar sulhu.”
Lokacin kawo karshen yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan lokacin da yake ganin za a kawo karshen yaki da Iran.
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa yana ganin yakin da ake yi da Iran zai ƙare nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng

