Sojoji Sun Samu Nasarar Cafke Mataimakin Fitaccen Jagoran 'Yan Bindiga da Matarsa

Sojoji Sun Samu Nasarar Cafke Mataimakin Fitaccen Jagoran 'Yan Bindiga da Matarsa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a kokarin da suke yi na yin fito na fito da 'yan bindigan da ke addabar mutane ta hanyar hana su zama lafiya
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar cafke wani mataimakin jagoran 'yan bindiga, Kachalla Auta, tare da matarsa a jihar Gombe
  • Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen biyu sun shiga hannu ne bayan samun bayanan sirri kan shirinsu na tserewa daga wani daji a jihar Plateau

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Dakarun sojoji sun kama mataimakin wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Auta, tare da matarsa a jihar Gombe.

Dakarun sojojin sun kama mutanen ne biyo bayan wani samame na musamman da aka gudanar ta hanyar amfani da bayanan sirri a wurare daban-daban.

Sojoji sun cafke mataimakin jagoran 'yan bindiga
Mataimakin jagoran 'yan bindiga da aka fi da Pakapaka da matarsa da sojoji suka cafke Hoto: @zagazolamakama
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki fada, sun yi garkuwa da mai martaba Sarki a Najeriya

An cafke mataimakin jagoran 'yan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin, waɗanda aka bayyana sunayensu da Bala, wanda aka fi sani da “Pakapaka,” da kuma matarsa Zulaiha Bala, bayan da suka tsere daga dajin Madami da ke jihar Plateau.

A cewar majiyoyin, kamen ya biyo bayan sa ido da dabarun leken asiri tare da bin sawun mambobin wannan gungun masu laifi da dakarun tsaro suka yi yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

Ana ci gaba da bincike

A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna tsare inda ake gudanar da bincike domin gano irin rawar da suke takawa a ayyukan rukunin da kuma alaƙar da ke tsakaninsu da sauran rassan ‘yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a cikin yankin da ma wajensa.

A wani labarin mai alaƙa da wannan, dakarun sojoji sun gudanar da sintiri a kewayen ƙauyen Bayar da ke yankin Duguri bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa babban jagoran ‘yan bindigan ya tsere zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban da suka je yin jarabawar JAMB

Sai dai, dakarun sojojin ba su haɗu da shi ba a yayin aikin binciken da suka gudanar.

Majiyoyin tsaro sun ce dakarun sun ci gaba da mamaye yankunan tare da dorewar sintiri da nufin hana masu aikata laifuffuka damar yin zirga-zirga tare da ruguza hanyoyin ayyukansu a jihohin Plateau da Taraba da kuma jihohin da ke maƙwabtaka da su.

Sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sahabi Abdulrahman ya yaba kan nasarar da dakarun sojojin suka samu wajen cafke hatsabibin dan bindigan.

"Wannan nasara ce babba, kuma muna yabawa dakarun sojoji kan namijin kokarin da suke yi wajen samar da tsaro."
"Allah ya ci gaba da tona asirin dukkanin mutanen da ke da hannu wajen hana jama'a zaman lafiya da kwanciyar hankali."

- Sahabi Abdulrahman

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

'Yan bindiga sun sace masu rubuta JAMB

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da fasinjoji da dama, ciki har da daliban da ke shirin zana jarabawar shiga jami'a (JAMB).

Lamarin ya auke ne kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo a jihar Benue lokacin da maharan suka tare wata motar bas ta kamfanin Benue Links.

Rahotanni sun nuna cewa motar na ɗauke da fasinjoji kusan 18, inda mafi yawancinsu matasa ne da ke kan hanyar zuwa Otukpo domin zana jarabawar JAMB.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng