Babbar Magana: Kotu Ta Umarci a Cafke Tsohuwar Ministar Buhari, an Ji Dalili
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) na yin shari'a da tsohuwar Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq
- Alkalin da ke jagorantar shari'ar ya ba da umarnin a cafke tsohuwar Ministar bayan ta gaza bayyana a gaban kotu
- Lauyoyin wadanda ake kara sun yi kokarin bayanin dalilin rashjn halartarsu zaman, amma alkalin kotun bai gamsu ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja da ke Apo ta ba da takardar umarnin kamo Sadiya Umar Farouq.
Kotun ta ba da umarnin ne domin cafke tsohuwar Ministar ta jin ƙai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma a lokacin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce alƙalin kotun, mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da umarnin kamo Bashir Nura Alkali, wanda shi ne babban sakatare a ma’aikatar.
Kotun ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan buƙatar da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin kasa ta’annati (EFCC) ta shigar.
Meyasa kotu ta ce a kamo Sadiya Farouq?
EFCC ta shigar da bukatar ne bayan da waɗanda ake ƙarar suka gaza bayyana a gaban kotun domin gurfanar da su kamar yadda aka tsara a yau Alhamis.
Wannan umarni ya biyo bayan rashin halartar waɗanda ake ƙaran a kotu domin amsa tuhume-tuhume guda 21 da hukumar EFCC ta shigar a kansu.
Yayin zaman kotun, lauyan masu ƙara, Rotimi Jacobs (SAN), ya shaida wa kotun cewa duk da an shigar da tuhumar ne tun ranar 15 ga Disamba, 2025, duka waɗanda ake ƙarar su biyu sun ƙi bayyana domin gurfanar da su.
Ya bayyana cewa rashin bayyanarsu ya sa hukumar EFCC na shan wahalar ba su takardar sammaci, inda ya lura cewa wanda ake ƙara na uku ne kawai, Sani Nafiu Mohammed, ya halarci kotun.
Jacobs ya ƙara da cewa ko da yake lauyoyi sun ba da tabbacin cewa waɗanda ake ƙarar za su zo, wanda ake ƙara na uku ne kawai ya amsa kiran da aka yi masa ta hannun wanda ya tsaya masa, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan
Kudurin hana Trump sayar wa Isra'ila bama bamai ya gamu da cikas a majalisar dattawa
Takaddama kan uzurin rashin lafiya
Lauyan EFCC ya nuna damuwa kan iƙirarin tsohuwar Ministar na cewa ba ta da lafiya, inda ya bayyana cewa a baya ma ta taɓa neman izinin tafiya ƙasashen waje domin neman magani.
A nasa ɓangaren, lauyan wadanda ake kara, Abdul Ibrahim (SAN), ya danganta rashin halartar wadda yake karewa ga matsalolin lafiya, inda ya roƙi kotun da ta karɓi takardar rantsuwa da ya shigar.
Sai dai alkalin kotun, mai shari'a Onwuegbuzie ya ƙi amincewa da wannan takarda.

Source: Facebook
Kotu ta amince a kamo su
Daga nan ne EFCC ta nemi umarnin kotu domin tilasta wa waɗanda ake ƙarar bayyana, tana mai kafa hujjar cewa sun gaza kiyaye sharuɗɗan belin da aka ba su.
Duk da roƙon da lauyan wadanda ake kara ya yi na a ba su ƙarin lokaci domin zuwa da tsohuwar Ministar, mai shari'aOnwuegbuzie ya amince da bukatar EFCC, inda ya ba da umarnin kamo waɗanda ake ƙarar su biyu nan take.
An ɗage saurarar ƙarar zuwa ranar Litinin, 18 ga Mayu, 2026, domin gurfanar da su.
Sadiya ta ki amsa gayyatar EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar Ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta ki amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi mata.
Hukumar EFCC ta yi mata gayyatar ne bisa binciken zargin halasta kudin haram da ya kai naira biliyan 37 a lokacin tana rike da mukami.
An gayyaci tsohuwar Ministan ne ta bayyana gaban masu bincike a hedkwatar EFCC don bada ba'asi kan zargin almundahar da aka yi a lokacin tana ofis.
Asali: Legit.ng

