Atiku ko Obi: An Yi Hasashen Wanda Zai Samu Tikitin ADC a Zaben 2027
- Ana ci gaba da muhawara kan dan takarar da zai iya samun tikitin jam'iyyar ADC a zaben shugaban kasa na 2027
- Wani jigo a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya yi hasashen dan takarar da zai iya samun tikitin na ADC mai adawa a Najeriya
- Segun Showunmi ya lissafo dalilan da suka sanya yake ganin Atiku Abubakar zai samu tikitin ADC domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Showunmi, ya yi magana kan dan takarar da zai samu tikitin ADC a zaben shugaban kasa na 2027.
Segun Showunmi ya bayyana kwarin gwiwa cewa Atiku Abubakar ne zai lashe tutar takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC gabanin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Segun Showunmi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027
Meyasa Atiku zai iya lashe tikitin ADC?
Showunmi ya bayyana dalla-dalla cewa Atiku yana da duk wani karsashi na zama ɗan takarar jam’iyyar.
Ya ce babu ko shakka a ransa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai samu tikitin ADC, yana mai nuni da ƙarfinsa na siyasa da kuma shirye-shiryensa na shiga tseren.
Sai dai, ya lura cewa Atiku na iya fuskantar takara mai zafi daga tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya bayyana a matsayin babban abokin hamayyar Atiku a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da ake sa rai.
Halin da Arewacin Najeriya ke ciki
Showunmi ya kuma yi tsokaci kan yanayin siyasar Najeriya baki ɗaya, inda ya nuna cewa akwai ƙaruwar rashin jin daɗi a tsakanin masu zaɓe, musamman a yankunan Arewa.
A cewarsa, duka al’ummomin karkara da na birane a Arewa suna cikin fushi da ɓacin rai, yanayin da yake jin zai taka rawar gani wajen tantance sakamakon zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya sanar da 'yan Najeriya sabon tsarin da zai kawo idan ya zama shugaban kasa
Ya gargaɗi ’yan siyasa game da halin watsi da amintattun abokan tafiya bayan sun ci moriyarsu, yana mai nuni da cewa irin wannan mataki na iya dawowa ya shafe su yayin da ake sake fasalin ƙawance gabanin zaɓen.
Wane shiri Atiku yake da shi
Da yake ƙara magana kan shirye-shiryen Atiku, Showunmi ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda ya ba da dukkan hankalinsa ga takarar, yana mai jaddada cewa a shirye yake ya fafata sosai.

Source: Facebook
Showunmi ya nuna yankin Kudu-maso-Gabas a matsayin muhimmin yanki da zai iya tantance wanda zai yi nasara, shafin Naijanews ya dauko labarin.
Sabanin haka, ya nuna shakkunsa kan yankin Kudu maso Yamma, inda ya bayyana tsarin zaɓen yankin a matsayin wanda ba a iya hasashensa.
Haka zalika, ya jaddada muhimmancin yankin Arewa ta Tsakiya, inda ya buƙaci ’yan siyasa su ɗauki damuwar yankin da mahimmanci, domin zai iya zama yanki mai matuƙar tasiri wajen karkata akalar zaɓen.
Hadimin Tinubu ya yi wa Atiku martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Alhaji Atiku Abubakar martani.
Daniel Bwala ya gayawa Atiku Abubakar cewa zai sake shan kaye a hannun jam’iyya mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Bwala ya ce tabbas Atiku ne zai kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, amma Tinubu zai sake doke shi kamar yadda ya yi a 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
