Rarara Ya Kira Ruwa, PDP Ta Yi Masa Tatas kan Taba Pantami

Rarara Ya Kira Ruwa, PDP Ta Yi Masa Tatas kan Taba Pantami

  • Jam'iyyar PDP a Gombe ta ce wakar Dauda Kahutu Rarara da ta ambaci Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na dauke da batanci da rashin mutuntawa
  • PDP ta zargi mawakin da kokarin bata sunan dan takararta na gwamna tare da cewa sabanin siyasa bai kamata ya zama hanyar cin mutuncin mutane ba
  • Jam'iyyar ta bukaci 'yan siyasa da magoya bayansu su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shirye gabanin zaben 2027 maimakon zage-zage

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe ta yi Allah wadai da kalaman da ta bayyana a matsayin batanci da fitaccen mawakin siyasa na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, ya yi wa dan takararta na gwamna, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Jam'iyyar ta ce kalaman da ke cikin wata waka da mawakin ya fitar kwanan nan sun kunshi bata suna, rashin mutuntawa, kuma an yi su ne da nufin tauye kyawawan dabi'u da ingantacciyar mu'amalar dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Ana wasan sauya sheka a Gombe, sakataren ADC ya yi murabus, ya kama layin Pantami

PDP ta soki Rarara kan taba Pantami
Mawaki Dauda Kahutu Rarara da Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Dauda Kahutu Rarara, Prof Isa Ali Pantami
Source: Facebook

PDP ta soki wakar Rarara

Q ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam'iyyar a jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar.

PDP ta ce sabanin siyasa bai kamata ya zama uzuri na cin mutunci ko bata sunan fitattun mutane ba.

Sanarwar ta kara da cewa Farfesa Pantami, wanda malamin addinin Musulunci ne kuma farfesa mai suna a fagen ilimi a duniya, ya cancanci a girmama shi ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba.

Sanarwar ta ce:

"Wakar ta kunshi bata suna kuma abin kunya ne ga al'adun kasa da manufofin dimokuradiyya. Ya kamata a mutunta manyan mutane tare da kare martabarsu."

PDP ta yi zargi kan kyaututtukan gwamnati

Jam'iyyar adawar ta kuma zargi Rarara da kasancewa yana da tarihin yin kalamai na cin mutunci kan wasu fitattun shugabanni, ciki har da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Bugu da kari, PDP ta yi zargin cewa sabon harin da mawakin ya kai na iya kasancewa yana da alaka da sukar da jam'iyyar ta yi wa gwamnatin jihar Gombe kan rahotannin bayar da motoci, filaye da kudade da darajarsu ta haura Naira miliyan 200 ga mawakin.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na tsaka mai wuya, jam'iyyar PDP ta yi bayani

Jam'iyyar ta jaddada cewa har yanzu tana kallon wadannan kyaututtuka a matsayin amfani da dukiyar al'umma ta hanyar da ba ta da hujja.

Kira ga mutunta juna a siyasa

PDP ta amince cewa mawaka da masu nishadantarwa na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama'a da shiga harkokin siyasa, amma ta yi gargadin kada a rika amfani da su wajen kai hare-haren kashin kai ko rura wutar rikicin siyasa.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Abin takaici ne idan masu fasaha suka bari a yi amfani da su wajen sasanta rikicin siyasa maimakon inganta zaman lafiya, hadin kai da kyakkyawar zamantakewa."
PDP ta kare Farfesa Pantami
Dan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Prof Isa Ali Ibrahim Pantami
Source: Facebook

Jam'iyyar ta yi kira ga shugabannin siyasa a dukkan jam'iyyu da su gargadi magoya bayansu da abokan huldarsu su guji furta kalaman da za su zagi abokan hamayya ko su kara rarrabuwar kawuna a cikin al'umma.

A karshe, PDP ta ce ya kamata yakin neman zaben 2027 ya ta'allaka ne kan batutuwan da suka shafi manufofi, tsare-tsare da hangen nesa, ba zage-zage da bata suna ba.

Batun Pantami ya wulakanta sarkin Gombe

Kara karanta wannan

Bayan shan suka Gwamna Abba ya kare matakin ba 'yan APC filaye sama da 1500

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar mai martaba sarkin Gombe ta yi martani kan batun cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya wulakanta sarki.

Fadar ta karyata zargin da ake yadawa cewa an hana Sarkin ganawa da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, lokacin da yake kan mukamin Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng