An Zo Wajen: Trump Ya Tsage Zance kan Cimma Yarjejeniya da Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya dauko batun yarjejeniyar da aka shirin cimmawa tsakanin kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Donald Trump ya nuna cewa Iran a shirye take ta yi abubuwan da watanni biyu da suka gabata ba za ta iya yinsu ba
- Shugaban na Amurka ya nuna kyakkyawan fatan cewa kasashen biyu za su cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin da ake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaba Donald Trump ya nuna kyakkyawan fata game da cimma yarjejeniya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Trump ya yi iƙirarin cewa Tehran a yanzu tana shirye ta aikata abubuwan da ba za ta iya yi ba watanni biyu da suka gabata.

Source: Twitter
Tashar CNN ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan nr yayin da yake magana da manema labarai a fadar White House ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Iran ta amince da bukatar Amurka, ta canza ahawara kan batun keramakamin nukiliya
Trump ya ce an cimma yarjejeniya da Iran
Ya ambaci cewa an cimma matsaya kan cewa ƙasar ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma za ta mika dukkan "kayan nukiliya" da take da ita.
Trump ya kuma yaba da yadda aka gudanar da aka tattauna kasashen Amurka da Iran.
“Babban abin da yake da mahimmanci shi ne Iran ba za ta samu makamin nukiliya ba, kuma sun amince da hakan. Iran ta amince da hakan, kuma sun amince da shi cikin kakkarfar murya."
"Sun amince za su ba mu kayayyakin nukiliya da ke can ƙarƙashin ƙasa sakamakon harin da muka kai musu da jiragen yaƙi na B2. Don haka muna da yarjejeniyoyi da dama da Iran."
- Donald Trump
Sai dai, har yanzu ƙasar Iran ba ta tabbatar da cewa ta amince da waɗannan sharuɗɗa ba.
Matsayar Trump kan makaman nukiliya
“Iran tana son yin yarjejeniya, kuma muna tattaunawa da su cikin mutunci. Dole ne su kasance ba su da makaman nukiliya."

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya yi maganar lokacin kawo karshen yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
"Wannan babban al’amari ne, kuma a yau suna shirye su aikata abubuwan da ba su shirya aikatawa ba watanni biyu da suka gabata.”
- Donald Trump

Source: Getty Images
Shin an sanya wa'adi ga Iran?
Yayin da aka tambaye shi game da shawarar da aka bayar a baya na cewa Iran ta dakatar da inganta sinadarin uranium na tsawon shekaru 20, Trump ya ce babu wani iyakacin lokaci na shekaru 20, kuma duk wata dakatarwa za ta wuce haka.
“Muna da wata sanarwa, sanarwa mai ƙarfi, cewa ba za su mallaki makaman nukiliya ba har bayan shekaru 20... babu wani iyakacin shekaru 20 a nan.”
- Donald Trump
Trump ya magantu kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan matakin da kasarsa ta dauka kan Iran.
Shugaba Donald Trump ya jinjinawa matakin da Amurka ta ɗauka na killace tashoshin jiragen ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaban na Amurka ya yi iƙirarin cewa matakin ya sa Iran ta gaza gudanar da kowane irin kasuwanci, yana mai nuni da abin da ya kira rugujewar ƙarfin sojinta baki ɗaya. R
Asali: Legit.ng