Manyan Labarai A Yau
Rundunar yan sandan jihr Legas ta ce bam din da aka dasa a wata mota ya tarwatse ne lokacin da aka yi yunkurin tayar da motar, mutum daya ya samu runi.
Bangaren gwamnatin tarayya na ci gaba da gabatar da shaidu a shari'ar da ake tuhumar Malam Nasir El-Rufai da kutse a wayar NSA Nuhu Ribdu a kotun tarayya.
Dan wasan gaba na Argentina, Lionel Messi, ya kafa tarihi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. Messi ya zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar.
Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani samame a maboyar 'yan ta'adda da ke jihar Katsina. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato manyan makamai.
Ministn ayyuka, David Umahi ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na zama da kamfanonin siminti domin duba yiwuwar rage tsadar da yake yi a Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben shekarar 2027, Peter Obi, ya yi kira ga mai girma Bola Tinubu ya sauka daga kan mukaminsa.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Jamilu Isiyaku Gwamna, ga Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar rashin tsaro.
Tsohon hadimin gwamnan jihar Gombe, Aliyu Musa, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP. Ya nuna goyon bayansa ga takarar Farfesa Isa Ali Pantami.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari