'Ba za Ta Sabu ba': Isra'ila Ta Yi Fatali da Shirin Amurka a Gaza
- Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ta yi watsi da shirin Amurka mai dokoki 15 kan samar da zaman lafiya a Gaza
- Bengajamin Netanyahu ya ce Isra’ila ba za ta janye dakarunta daga Gaza ba har sai Hamas ta mika makamanta gaba ɗaya
- Ya kuma ce matuƙar yana kan kujerar firaminista, ba zai amince da kafa ƙasar Falasɗinawa kamar yadda wasu ke fafutuka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Israel – Benjamin Netanyahu, ya ce ƙasarsa ta yi watsi da shirin Hukumar Zaman Lafiya na Shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza da ke Falasdinu.
Ya nanata cewa Isra’ila ba za ta janye dakarunta daga yankin Hamas da ake yi wa mulkin kama karya ba har sai ƙungiyar Hamas ta ajiye makamanta gaba ɗaya.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta kawo labarin cewa Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar ministocin Isra’ila a ranar Lahadi, 9 ga qatan Agusta, 2026.
Isra'ila ta yi watsi da shirin Amurka
CNN ta ruwaito cewa Netanyahu ya ce rundunar sojin Isra’ila ba za ta aiwatar da wani shirin janye dakarunta ba har sai Hamas ta ajiye makamanta da gaske.
Ya ce:
“Isra’ila ta yi watsi da wannan takarda mai dokoki 15.” Kuma za ta ci gaba da dakile barazanar da ake yi wa dakarunmu da kuma al’ummarmu.”
Netanyahu ya ƙara da cewa Isra’ila tana tattaunawa da Amurkawa kan wannan batu, amma su na nan a kan bakarsa.
Isra'ila na kai hari Gaza
Ya zuwa yanzu, Fadar White House da Hamas ba su fitar da martani nan take kan kalaman Netanyahu ba na cewa ba gudu ba ja da baya ba.
Isra’ila ta ci gaba da kai hare-haren da ke haddasa asarar rayuka kusan kullum a sassa daban-daban na Gaza tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a watan Oktoban 2025.

Source: Getty Images
A ranar 30 ga watan Yuli, 2026 Trump ya sanar da abin da ya kira yarjejeniyar tarihi, wadda ta ƙunshi ajiye makaman Hamas da dukkan sauran ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Gaza.
Trump ya bayyana hakan a matsayin babban mataki zuwa ga samar da zaman lafiya da tsaro na dindindin.
Sai dai a makon da ya gabata, Hukumar Zaman Lafiya da Amurka ke jagoranta ta ce janyewar sojojin Isra’ila daga Gaza ba za ta faru ba har sai an kammala ajiye makaman Hamas.
Amurka ta nemi alfarma a Iran
A baya, mun wallafa cewa Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya ce Amurka na neman Iran ta yi alkawarin ba za ta kara harbin jiragen ruwa na kasuwanci ba.
Vance ya ce dole a kwashe nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigar ruwan Hormuz domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin tsaro ba tare da an mai masu hari ba.
Adadin jiragen ruwa da ke ratsa mashigar ya yi matukar raguwar bayan takaddama da hare-haren da suka shafi Iran da Amurka, musamman game da iko da Hormuz.
Asali: Legit.ng


