"Za a Kore Shi"; Amaechi Ya Kalubalanci Tinubu da Ya Yi Abu 1 kan Zaben 2027
- Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, na daga cikin masu son samun takara a jam'iyyar ADC domin fafatawa da shugaban kasa Bola Tinubu
- Rotimi Amaechi ya fito ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda tattalin arzikin kasar nan ya tabarbare
- Tsohon Ministan ya nuna cewa 'yan Najeriya da dama sun kosa domin kawar da Shugaba Tinubu a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana shirin da 'yan Najeriya suke da shi kan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Amaechi ya bayyana cewa ’yan Najeriya da dama suna ɗokin ganin sun kori Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki a zaɓen shekarar mai zuwa.

Source: Twitter
Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Afirilun 2026 a shirin The Morning Brief na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Saraki ya jefi gwamnatin Buhari da zargi kan fashin Offa, ya fallasa gwamnan Kwara
Amaechi ya soki gwamnatin Tinubu
Amaechi ya bayyana tabarbarewar yanayin tattalin arziƙi da ƙaruwar wahalhalu a faɗin ƙasar a matsayin dalilansa.
“Kowa yana wahala, kowa yana neman abinci. Mutane ba za su iya siyan man fetur ba, ba za su iya yin tafiya ba. Kamfanonin jiragen sama suna barazanar ƙara kuɗin sufuri; komai ya tashi sama.”
“Don darajar Ubangiji, Shugaba Tinubu ba shi da haƙƙin yin magana, ba shi da shi. Ya yi alƙawarin wutar lantarki kuma ya ce idan bai bayar da wuta ba, kada mutane su zaɓe shi. ’Yan Najeriya suna jiran su kore shi (daga kan mulki).”
- Rotimi Amaechi
Batun kabilanci a siyasar Najeriya
Tsohon ministan sufurin ya kuma soki yadda ake amfani da ƙabilanci da addini wajen zaɓin siyasa a Najeriya, yana mai nuna cewa irin waɗannan ra’ayoyin su ne suka taimaka wajen kawo yanayin da ake ciki yanzu.
“Na gayawa ’yan Najeriya, ku bar batun ƙabila da addini, su ne suka kawo mu nan. Waɗanda suka taimaka wa Shugaba Tinubu ya zama shugaban ƙasa sun biyo manufar addini ne."

Kara karanta wannan
Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa
"A yau, sun gano cewa kasuwa ba ta san Kirista ko Musulmi ba; kasuwa yare ɗaya kawai ta sani, wato Naira da Kobo."
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Amaechi ya kalubalanci shugaba Tinubu
Haka zalika, Amaechi ya yi zargin katsalandan a hukumomin dimokuraɗiyya, inda ya ce gwamnati tana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa gabanin zaɓe mai zuwa.
“Ko zaɓen ya kasance na adalci ko akasin haka, muddin mu (ADC) muna cikin takardar zaɓe, Shugaba Bola Tinubu zai fadi zaɓe. Matsalar ita ce baya son wani ɗan takara mai ƙarfi ya bayyana a takardar zaɓen.”
Idan Tinubu yana da yakinin zai yi nasara a 2027, gaya masa ya gayawa Nuhu Ribadu ya fita daga harkar bangaren shari’a da hukumar INEC."
Idan yana tunanin yana da ikon cin zaɓen, su bar INEC da ɓangaren shari’a su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma baki ba."
- Rotimi Amaechi
Jagoran ADC, Amaechi ya ba ADC shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Rotimi Chibuike Amaechi, ya bayar da shawara ga jam'iyyar ADC kan zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan
Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027
Amaechi ya buƙaci jam’iyyar ADC da ta zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa mai inganci wanda zai iya lallasa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Tsohon Ministan ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji la’akari da ƙabila ko addini yayin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng