Amurka Ta Cimma Yarjejeniya da Iran kan Shirin Kera Makamim Nukiliya, Trump Ya Yi Bayani

Amurka Ta Cimma Yarjejeniya da Iran kan Shirin Kera Makamim Nukiliya, Trump Ya Yi Bayani

  • Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta amince ba za ta kera makamim nukiliya ba har abada kuma ba tare da gindaya wani sharadi ba
  • Trump ya bayyana haka ne yayin da ake rade-radin cewa Amurka ta amince za ta saki wasu kadarorin Iran da ta rike a baya
  • Wannan na zuwa ne yayin da kasashen biyu ke ci gaba da tattaunawa domin samun matsaya, wacce ake fatan ta dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince da dakatar da shirinta na nukiliya na har abada.

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni daga bangarorin Amurka da Iran ke nuna cewa an kama hanyar cimma matsayar zaman lafiya a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Iran ta kafe kan sharadin sulhu da Amurka, ta yi fatali da tsagaita wuta na wucin gadi

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin hira da menama labarai a Washington DC Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Shugaba Trump ya kuma sanar da cewa da yiwuwar a sake komawa birnin Islamabad na kasar Pakistan don karkare wannan yarjejeniya.

Yadda Amurka da Iran suka fara zama

Tun a taron farko da ya gudana a karshen makon da ya gabata, Amurka da Iran sun samu sabani kan batutuwa da dama, amma wanda ya fi shahara shi ne batun shirin nukiliya.

Yayin da Amurka ta dage cewa ba za ta yarda Iran ta ci gaba da shirin kera makamim nukiliya ba, kasar Musulunci ta nanata cewa shirinta ba na kera makami ba ne, na zaman lafiya ne.

Bayan tashi baram-baram a taron farko, an ruwaito cewa Amurka da Iran sun ci gaba da tattaunawa da juna ta bayan fage domin warware wuraren da suka samu sabani.

Iran ta dakatar da shirin nukiliya

Da yake karin bayani kan batun shirin nukiliyan Iran yau Juma'a, 17 ga watan Afrilun 2026, Shugaba Trump ya nuna alamun cewa suna dab da cimma yarjejeniya.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya tsage zance kan cimma yarjejeniya da Iran

Trump ya ce a halin da ake ciki Iran ta amince za ta dakatar da shirinta na kera makamim nukiliya har abada kuma ba tare da wani sharadi ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kasar ya kuma musanta rade-radin cewa Amurka ta amince za ta saki kadarorin Iran da suka kao datajar Dala biliyan 20, inda ya ce babu wata maganaai kama da haka.

Mojtaba Khamenei.
Jagoran addinin kasar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Sai dai, kamar yadda aka saba a irin wadannan lokuta, babu wani sahihin bayani daga bangaren Iran da ya tabbatar da wannan iƙirari.

Rahotanni sun nuna cewa irin wadannan kalamai daga Trump sun sha fitowa a baya, amma ba koyaushe ake samun daidaito da abin da Iran ke fada ba.

Iran ta bude mashigar ruwa ta Hormuz

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta sanar da bude mashigar ruwa ta Hormuz bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Labanon.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan, inda ya sanar da cewa an bude mashigar ruwa ta Hormuz gaba daya.

Abbas Araghchi ya kara da cewa duk jiragen kasuwanci za su iya wucewa ta mashigar cikin tsari da hukumomin jiragen ruwa na Iran suka tsara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262