Hatsabibin Ɗan Bindiga, Aliero Ya Rasa Ɗansa, Ƴan Uwa 8 yayin Arangama a Katsina
- Hatsabibin dan bindiga, Ado Aleiro ya gamu da cikas yayin da aka yi arangama da miyagu a jihar Katsina
- Aliero ya rasa ɗansa da wasu ’yan uwansa takwas, yayin da aka lalata babura kusan 30 na ƙungiyarsa a wani artabu a Katsina
- Rahotannin leƙen asiri sun ce asarar ta raunana bangaren Aleiro, tare da rage masa damar zirga-zirga, sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - An ruwaito cewa fitaccen ɗan bindiga Ado Aleiro ya fuskanci babban koma-baya yayin artabu a jihar Katsina.
Majiyoyi suka ce dan bindigar ya rasa ɗansa, wasu ’yan uwa takwas da babura kusan 30 a Katsina.

Source: Facebook
Bayanai daga Zagazola Makama ya samu sun nuna cewa asarar ta raunana ƙarfin gudanar da ayyuka da kuma zirga-zirgar ƙungiyar masu aikata laifuka ta Aleiro.
A cewar rahoton leƙen asirin mai kwanan watan 9 ga Agusta, dukkan babura kusan 30 da ƙungiyar ta yi amfani da su a artabun ba su dawo ba, yayin da aka ce an kashe waɗanda suke amfani da su.
Rahoton ya ƙara da cewa Aleiro ya rasa ɗansa da wasu ’yan uwa takwas a yayin artabun.
Ana kallon wannan a matsayin babban koma-baya ga ɗan bindigar, musamman saboda babura na da muhimmiyar rawa wajen zirga-zirga, sadarwa da gudanar da ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a Arewa maso Yamma.
Bayan asarar da aka ruwaito, bayanan leƙen asiri sun nuna cewa ya zuwa ƙarfe 3:51 na yammacin Lahadi, Aleiro yana tafiya shi kaɗai a babur a yankunan Sakya Dutse, Higi da Asaula.
Majiyoyi sun ce ana bibiyar motsinsa yayin da ake ƙoƙarin gano inda zai dosa na gaba da kuma tantance halin da ragowar hanyoyin sadarwar ƙungiyarsa suke ciki.
Wasu bayanan leƙen asiri sun kuma nuna cewa ɗan bindigar na nuna damuwa game da rashin tsaron wani wuri da aka shirya gudanar da ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Gidan Buhari, ƙarƙashin Chadiya Ward a ƙaramar hukumar Tsafe ta Zamfara.
An ruwaito cewa Aleiro na fargabar cewa ’yan Yansakai da ke aiki daga garin Tsafe za su iya kai hari kan wurin.
Ana ganin wannan fargaba na da alaƙa da raunin ƙungiyarsa bayan asarar da aka ruwaito a Katsina, da kuma yiwuwar tona asirin sauran hanyoyin gudanar da ayyukanta.
Majiyoyin tsaro sun ce sabon ci gaban na iya bai wa hukumomin tsaro damar ƙara matsa lamba kan ƙungiyar da ta raunana, tare da hana waɗanda suka tsira sake haɗa ƙarfi.
Musamman, lalata baburan na da muhimmiyar ma'ana, saboda hakan na iya rage ikon ƙungiyar wajen yin saurin zirga-zirga, kai hare-hare, jigilar kayayyaki da tserewa daga jami’an tsaro a wurare masu wahalar shiga.
Yaran AAdo Aliero suna arangama da ɗan bindiga
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa a cikin kwanaki biyu da suka gabata, an ce mabiyan Ado Aleiro na bibiyar Kachalla Muhammadu.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu na kara tsananta, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a yankunan.
Wasu na ganin wannan rikici ya rage matsin lamba kan al’ummomi, domin bangarorin na raunana junansu maimakon kai hare-hare ga fararen hula.
Asali: Legit.ng

