Jang: Dalilin da Ya Sanya Rikicin Jihar Filato Ya Ƙi ci Ya Ƙi Cinye wa

Jang: Dalilin da Ya Sanya Rikicin Jihar Filato Ya Ƙi ci Ya Ƙi Cinye wa

  • Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang, ya ce rikicin jihar ya samo asali ne daga matsalolin tarihi, siyasa, ƙasa, adalci da batun ‘yan asali da ‘yan ƙasa
  • Jang ya bayyana wasu dalilai da suka jawo rikicin ya ki zuwa garshe da suka hada da gazawar shugabanni a daukar matakan da suka dace
  • Tsohon gwamnan ya ce Plateau na buƙatar sulhu, warkarwa da sake gina jihar baya ga matakan tsaro domin kawo ƙarshen rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin labarai, siyasa da al'amuran yau da kullum, wanda ke da gogewa wajen nazarin al'amuran da suka shafi Najeriya

Plateau – Tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Jonah David Jang, ya bayyana dalilin da ya sa rikicin da ya addabi jihar tsawon shekaru bai samu cikakken magani ba.

A cewar tsohon gwamnan, gazawar shugabannin jihar da rashin magance matsalolin da ke ƙasa tun farko sun taimaka wajen tsawaita rikicin.

Jonah Jang ya yi magana kan rikicin da aka dade ana yi a Filato.
Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah David Jang. Hoto: Jonah Jang
Source: Facebook

Tushen rikici a jihar Filato

Kara karanta wannan

An samu afkuwar ambaliya a Arewa, gidaje da wasu muhimman kadarori sun lalace

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe daruruwan mutane a hare-haren rikice-rikicen da suka faru a sassa daban-daban na jihar tun shekarar 2001, yayin da aka lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira tare da raba mazauna wasu yankuna da muhallansu.

Rikicin ya ci gaba da shafar garuruwa daban-daban na Plateau tsawon sama da shekaru 20, inda hare-hare da ake kai wa lokaci-lokaci ke haifar da asarar rayuka da gudun hijirar jama'a.

Jang ya bayyana matsayinsa ne a cikin sabon littafinsa mai suna From Airman to Politics: My Life, wanda aka kaddamar a Jos ranar 1 ga watan Agustan 2026.

Tsohon gwamnan ya ce tushen rikicin Plateau ba wai batun tsaro kaɗai ba ne, yana da alaƙa da batutuwan tarihi da na siyasa da suka shafi mallakar ƙasa, adalci, asali da kuma damar zama cikakken ɗan jihar.

Ya ce:

“Idan na waiwayi tushen rikicin da ya mamaye Jihar Plateau, ina ganin wani bala'i ne na tarihi da kuma wanda mutane suka haifar. Wata guguwa ce da ta kwashe shekaru tana tasowa, amma aka bari ta barke saboda jerin gazawa wajen shugabanci da gudanar da mulki.”

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: An rufe makarantu 65 a Sokoto, Katsina da wasu jihohin Arewa

A cewarsa, wasu daga cikin matsalolin sun haɗa da koke-koke da ba a magance su ba, tashin hankali da aka yi watsi da shi, tauye haƙƙoƙi da kuma rashin adalci da ya samu gindin zama.

Batun ‘indigene’ da ‘citizenship’

Jang ya ce batun bambancewa tsakanin ɗan asalin Plateau da wanda yake zama a jihar ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa rikicin.

Ya ce an dade ana fama da tambayoyi kan wanda ke da ikon mallakar ƙasa, wanda zai iya tsayawa takarar zaɓe da kuma wanda za a ɗauka a matsayin cikakken ɗan Plateau.

“Tambayar ɗan asali da ɗan ƙasa ta kasance tana damun jiharmu. Wa ke da ikon mallakar ƙasa? Wa ke da ikon tsayawa takarar zaɓe? Wa ke da ikon a kira shi ɗa ko ‘yar Plateau?
“Waɗannan tambayoyin sun ci gaba da taruwa cikin shiru har sai da suka rikide zuwa zubar da jini.”

A cewar Jang, rashin magance waɗannan batutuwa tun da wuri ya taimaka wajen haifar da yanayin da rikicin ya samu damar ci gaba.

Jang ya soki gwamnatocin baya

Jang, wanda ya taɓa zama gwamnan mulkin soja na jihohin Benue da Gongola, ya zargi gwamnatocin da suka biyo baya da kasa ɗaukar matakan da suka dace wajen magance rikicin Plateau.

Kara karanta wannan

"Mun bar ku da Allah': Mazauna Sokoto sun tura sako ga Gwamna kan rashin tsaro

Tsohon gwamnan ya ce matakan da aka ɗauka ba su kasance masu cikakken tasiri wajen warware matsalolin da suka dade suna rura wutar rikicin ba.

Ya nuna cewa samar da tsaro kaɗai ba zai wadatar wajen magance matsalar ba, domin akwai buƙatar a magance abubuwan da ke haddasa rashin jituwa tsakanin al'ummomin jihar.

Tsohon gwamna, Jonah Jang ya yi magana game da matsalar tsaro a Filato
Taswirar jihar Filato, inda rahotanni suka ce tana fuskantar matsalar tsaro. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya buƙaci sulhu da sake gina jihar

Jang ya ce Plateau na buƙatar matakan da suka wuce samar da jami'an tsaro domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

A cewarsa, jihar na buƙatar warkar da raunin da rikice-rikicen suka haifar, sulhu tsakanin al'ummomin da ke rikici da kuma sake gina wuraren da aka lalata.

Ya ce:

“Abin da Plateau ke buƙata kuma har yanzu take buƙata ba tsaro kaɗai ba ne, har da warkarwa. Ba sake gini kaɗai ba, har da sulhu.
“Dole ne mu koma kan teburin tattaunawa mu tambayi kanmu: Mene ne ma'anar kasancewa ɗan Plateau? Ta yaya za mu raba ƙasa, iko da damammaki ta hanyar da za ta mutunta tarihi tare da tabbatar da daidaito?”

Tsohon gwamnan ya ce waɗannan tambayoyi ba a magance su yadda ya kamata ba a shekarun da aka shafe ana fama da tashin hankali, kuma hakan na daga cikin dalilan da ya sa rikicin ya ci gaba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya jawo cece kuce bayan ya yi wasu kalamai

Jang ya jaddada cewa samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin Plateau na buƙatar haɗa matakan tsaro da shirye-shiryen sulhu, adalci da sake gina al'umma domin dawo da zaman lafiya da amincewa tsakanin mazauna jihar.

An gano wuraren kera makamai a Filato

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun samu nasarar gano wasu wurare da ake kera makamai a cikin jihar Filato da ke fama da rikice rikice.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun samu nasarar kama mutane biyar tare da ƙwace bindigu da kayan aikin ƙera makamai a kamfanonin.

Sojoji sun ce suna ci gaba da farautar sauran makamai da harsasai da ke hannun miyagun yayin da ake kokarin shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com