Shugaba Donald Trump Ya Fadi Sharadin da Iran Ta Amince da Shi ana Shirin Sake Zama

Shugaba Donald Trump Ya Fadi Sharadin da Iran Ta Amince da Shi ana Shirin Sake Zama

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan bude mashigar Hormuz da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi
  • Donald Trump ya bayyana abin da Iran ta amince da shi kan mashigar Hormuz wadda ta rufe tun farkon fara yaki a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
  • Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa ba za a sake yin amfani da mashigar Hormuz ba a matsayin makami kan duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana abin da Iran ta amince da shi yayin da ake ta kokarin kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump ya yi iƙirarin cewa ƙasar Iran ta amince ba za ta sake rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz ba har abada.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Trump ya fadi abin da Iran ta yarda da shi
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Win McNamee
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Juma'a, 17 ga watan Afirilun 2026.

Me Trump ya ce Iran ta amince da shi?

Trump ya bayyana cewa ba za a sake amfani da mashigar Hormuz a matsayin makami kan duniya ba.

"Iran ta amince ba za ta sake rufe mashigar Hormuz ba. Ba za a sake yin amfani da ita (mashigar) a matsayin makami a kan duniya ba!”

- Donald Trump

Iran ta bude mashigar Hormuz

Tun da farko Trump ya sanar da cewa Iran ta bude mashigar Hormuz bayan ta rufe ta sakamakon yakin da aka fara tsakaninta da Isra'ila da Amurka.

Shugaban ya ce a halin yanzu mashigar ta Hormuz tana buɗe baki ɗaya kuma a shirye take don kasuwanci.

Sai dai Trump ya jaddada cewa killace hanyoyin ruwan Iran da sojojin Amurka ke yi zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniya da ƙasar.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris": Trump ya faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙi da Iran

“Killace hanyoyin ruwan zai ci gaba da kasancewa da cikakken ƙarfinsa ga Iran kaɗai, har sai lokacin da cinikinmu da Iran ya kammala 100%."

- Donald Trump

Trump ya ƙara da cewa wannan tsari “ya kamata ya tafi cikin sauri” tun da an riga ana tattaunawa kan yawancin muhimman batutuwa.

Trump ya ce an bude mashigar Hormuz
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Rashin tabbaci daga bangaren Iran

Tashar Aljazeera ta ce har yanzu babu wani tabbaci daga ɓangaren Iran game da iƙirarin Trump na cewa ba za su sake rufe mashigar ba, ko kuma za su miƙa sinadarin uranium da suka inganta mai ƙarfin gaske.

Bayanai daga majiyoyi sun nuna cewa ana kan shirye-shiryen komawa tattaunawa zagaye na gaba, wanda ya haɗa da tsarin wucin gadi na kwanaki 45 zuwa 60 wanda zai duba batutuwa da dama, ciki har da makomar sinadarin uranium da Iran ta inganta.

Trump ya magantu kan yakin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan lokacin kawo karshen yaki da Iran.

​Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa komai yana tafiya sumul kan yakin da aka fara a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Hakazalika, Shugaba Donald Trump ya ce ana sa ran yakin Iran zai zo ƙarshe a nan kusa-kusa ba da jimawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng