Gwamna Bala Ya Soke Batun Komawa Jam'iyyar APC, an Ji Dalili
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi tattaunawa da jam'iyyar APC da nufin sauya sheka zuwa cikinta
- Tattaunawar bangarorin biyu ba ta haifar da abin da ake zato ba, inda gwamnan ya fasa sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya
- Shugaban PDP na jihar Bauchi ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta ki amincewa da bukatar da suka gabatar mata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, daga jam’iyyar PDP zuwa APC ya ruguje biyo bayan rashin jituwa kan tsarin rabon madafun iko.
Tattaunawar da aka gudanar tsakanin gwamnan da ɓangarensa na PDP da kuma shugabancin APC ta ƙare ba tare da cimma matsaya ba.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce shugaban tsagin PDP karkashin jagorancin Turaki, Samaila Burga, ne ya bayyana hakan yayin yake magana da manema labarai ranar Asabar, 18 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027
Meyasa Gwamnan Bauchi fasa komawa APC?
Fasa sauya shekar ya biyo bayan kin amincewar da jam’iyya mai mulki ta yi da tsarin 60-40 na ikon kula da tsarin jam’iyyar a jihar Bauchi.
Sakamakon haka, gwamnan da magoya bayansa sun bayyana cewa a shirye suke su tattauna da sauran jam’iyyun siyasa, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
APC ba ta shirya karɓar Bala Mohammed ba
Shugaban na PDP a jihar, Sama’ila Burga, ya ce APC ta nuna cewa ba ta shirya karɓar tsarin PDP da kuma gwamnatin jihar ba.
Burga ya bayyana cewa APC ce ta fara buɗe tattaunawar ta hannun gwamnan, inda shugabannin jam’iyyar na ƙasa da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, suka ziyarci Bauchi domin lallashin Bala Mohammed ya shigo jam’iyyar tasu.
Ya bayyana cewa tattaunawar ta tsaya ne bayan da APC ta gaza amincewa da tsarin rabon kaso 60 ga gwamna da kuma 40 ga 'yan jam'iyyar (60-40), wanda ya lura cewa an yi amfani da irin wannan tsari a wasu jihohin da gwamnoni suka sauya sheƙa zuwa APC.

Kara karanta wannan
Wutar rikici ta fara tashi a jam'iyyar APC, Yilwatda ya gargadi tsafaffin ƴan PDP
“Haka aka yi a wasu wuraren da gwamnoni suka koma APC. Sun ƙi amincewa da wannan tsari, don haka mun rufe waccan tattaunawar. Ba za ka sa ran gwamnati da take tsarinta tun daga matakin mazaɓa har zuwa jiha ba ta da ikon kula da jam’iyyar ba."
- Samaila Burga

Source: Twitter
Gwamna Bala na neman wata jam'iyyar
Burga ya ƙara da cewa sun kira taron manema labarai ne bisa umarnin Mai girma Gwamna, wanda shi ne ke jagorantar tattaunawar.
Ya ce bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki, ɓangaren na PDP ya yanke shawarar dakatar da maganar komawa APC.
“Bayan yin nazari sosai, ya bayyana sarai cewa sharuɗɗan da mu ka gabatar domin sauya sheƙar ba su samu karɓuwa a wurin shugabancin APC ba. Ganin haka, muna son sanar da cewa tattaunawar ba ta haifar da ɗa mai ido ba, don haka an dakatar da ita a hukumance."
- Samaila Burga
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu suna bincika sauran jam’iyyun siyasa da za su iya komawa.
Gwamna Bala ya ba sarakuna motoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya raba motocin aiki ga sarakuna.
Motocin da aka raba sun hada da sababbin motocin saloon na GMC 14, bas-bas na Toyota, motocin daukar kaya na Hilux, da kuma fiye da motoci 100 kirar Toyota Camry.
Gwamna Bala ya bayyana cewa rabon motocin wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na karfafa shugabanci a matakin kasa da kuma bunkasa hulda da al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng