Atiku Ya Fadi Jam'iyyar da Za Ta Iya Kayar da APC a Zaben 2027

Atiku Ya Fadi Jam'iyyar da Za Ta Iya Kayar da APC a Zaben 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya karbi bakuncin shugabannin ADC na jihar Adamawa
  • Atiku ya bayyana jam'iyyar ADC a matsayin wadda ta shirya karbe mulki a hannun APC mai mulki a zaben 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ba shugabannin shawarar da su rungumi hadin kai tare da tafiya da kowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ita ce kaɗai jam'iyyar adawa da take a shirye don fuskanta tare da doke jam’iyyar APC mai mulki, wadda ya kira jam’iyya mai gazawa a babban zaɓe mai zuwa.

Atiku ya hango nasarar ADC a zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, 18 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi: An yi hasashen wanda zai samu tikitin ADC a zaben 2027

Me Atiku ya ce kan ADC?

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kwatanta ADC a matsayin jam’iyyar da take da “ingantattun manufofi da kuma tsari mai ƙarfi.”

“Ina nan daram kan yakinin cewa ADC ta zama sahihiyar tawagar adawa a Najeriya, wadda take da ƙarfin manufofi, tsari, da jajircewa, kuma a shirye take ta kalubalanci tare da doke APC wadda ta gaza a zaɓubbuka masu zuwa."

- Atiku Abubakar

Atiku ya karbi bakuncin shugabannin ADC

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ya karɓi baƙuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa a gidansa da ke Abuja ranar Juma’a, inda ya bayyana ziyarar a matsayin abin “taɓa zuciya.”

“Na gode musu bisa wannan karramawa, sannan na tunatar da sabon shugabancin jiha cewa haɗin kai shi ne babban aikin da ke kansu. Su dinke ɓarakar da ke akwai, su tafi da kowa, kuma su jagoranci mutane cikin adalci."

- Atiku Abubakar

Atiku ya yi magana kan jam'iyyar ADC
Atiku Abubakar tare da shugabannin ADC na Adamawa Hoto: @atiku
Source: Twitter

ADC ta ragargaji Tinubu

Kara karanta wannan

Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027

Kalaman Atiku na zuwa ne bayan sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun ƙudiri aniyar kaɗa Shugaba Bola Tinubu daga mulki a 2027.

Bolaji Abdullahi ya yi zargin cewa manufofin Shugaba Tinubu sun lalata rayuka da hanyoyin samun kuɗin shiga na jama’a.

Sakataren yada labaran na ADC ya yi martani ne ga kalaman da shugaban ƙasan ya yi a fadar gwamnati yayin da ya karɓi baƙuncin wasu jakadun Renewed Hope Ambassadors.

A wajen taron, Tinubu ya ce ba ya jin tsoron haɗuwar ƙungiyoyin adawa gabanin zaɓen 2027.

Sai dai, Abdullahi ya ce waɗannan kalamai sun nuna yadda shugaban ya nesanta kansa da zahirin wahala, rashin tsaro, da kuma takaicin da miliyoyin ’yan ƙasa suke ciki.

'Yan Kwankwasiyya sun yi wa Atiku martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani ga Atiku Abubakar kan kalaman da ya yi a kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwasiyya ta yi watsi da kalaman Atiku Abubakar, da ke nuna cewa tasirin siyasar Rabiu Musa Kwankwaso a Kano ya ja baya.

Kungiyar ta ce ikirarin Atiku ba gaskiya ba ne, inda ta nuna cewa mutum biyu kacal ne ke da mabiyan da ke kaunarsu da zuciya a fadin kasar nan, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng