Atiku Ya Kare Kansa kan Zargin Cin Hanci, Ya Tuna Baya kan Abin da Obasanjo Ya Yi Masa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiki Abubakar, ya kare kansa kan yawan danganta shi da zargin cin hanci da rashawa da ake yi
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu wata kwakkwarar shaida da ke nuna gaskiyar zarge-zargen da ake yi
- Tsohon mataimaki shugaban kasar ya tuna yadda aka kafa kwamiti a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo domin a bincike shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan jifarsa da ake yi da zargin cin hanci da rashawa.
Atiku ya bayyana cewa Olusegun Obasanjo, ya taɓa ba da izinin kafa wani kwamiti domin bincikarsa lokacin da yake kan mulki, inda ya ce binciken bai gano wata shaida ta cin hanci da rashawa a kansa ba.

Source: Twitter
Atiku ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2206 a shirin Prime Time na tashar Arise News.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya sanar da 'yan Najeriya sabon tsarin da zai kawo idan ya zama shugaban kasa
A yayin shirin, Atiku ya amsa tambayoyi kan daɗaɗɗen zarge-zargen da ake yi wa mutuncinsa.
An kafa kwamiti don bincikar Atiku
A cewarsa, an kafa kwamitin binciken ne a ƙarƙashin tsohon babban lauyan gwamnati Bayo Ojo (SAN), kuma ya haɗa da fitattun mutane kamar, Nuhu Ribadu, da kuma tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
“Tsohon shugabana, Olusegun Obasanjo, ya samu kowace dama. Ya kafa kwamiti a ƙarƙashin tsohon babban lauyan gwamnati Bayo Ojo. Nuhu Ribadu mamba ne, El-Rufai mamba ne."
- Atiku Abubakar
Ya bayyana cewa duk da yana da rigar kariya ta tsarin mulki a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa a wancan lokacin, ya janye wannan kariya da kansa domin ba da damar gudanar da binciken.
“Kuma sun zo ofishina, suka ce, ‘muna da umarni daga shugaban kasa na mu bincike ka.’ Na ce, ‘amma kun san ina da kariya ta tsarin mulki?’ Suka ce, ‘E.’ Na ce, ‘To, na yanke shawarar janye wannan kariya, ku bincike ni,’."

Kara karanta wannan
"Duk na kere su": Atiku ya kwatanta farin jininsa da na Kwankwaso, Tambuwal a Arewa
Ba a samu komai a kansa ba
Atiku ya jaddada cewa sakamakon binciken ya wanke shi daga kowane irin laifi.
“Sun bincike ni. Me suka samu? Babu komai!”
- Atiku Abubakar
Me Atiku ya ce kan zargin cin hanci
Ya ci gaba da cewa zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka biyo shi tsawon shekaru sun samo asali ne daga siyasa maimakon kwararan shaidu.
“Fahimtar da ake yi cewa ni mai cin hanci ne ta taso ne kawai ta hanyar zarge-zargen da ba a tabbatar da su ba."
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Da yake bayyana wannan lamari a matsayin wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, cewa shugaban ƙasa mai ci zai ba da izinin bincikar mataimakinsa, ya ce:
“Ina faɗar haka ne a karon farko a gaban jama’a, shugaban ƙasa ya kafa kwamiti don bincikar mataimakinsa wanda yake da kariya.”
Atiku zai samu tikitin ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya yi hasashen Atiku Abubakar zai samu tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a 2027.
Segun Showunmi ya bayyana dalla-dalla cewa Atiku yana da duk wani karsashi na zama ɗan takarar jam’iyyar.
Jigon na PDP ya ce babu ko shakka a ransa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai samu tikitin ADC, domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng
