Shari'a Ta Dawo Sabuwa: Saraki da Tsohon Gwamnan Kwara Za Su Gurfana a Kotu kan Fashin Offa
- Gwamnatin jihar Kwara ta sake dauko batun shari'ar fashi da makamin da aka yi a garin Offa wanda ya jawo asarar rayuka
- A cikin wadanda za su gurfana a gaban kotu akwai tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed
- Bukola Saraki ya sha nanata cewa zarge-zargen da ake yi masa kan fashin wani bita da kulli ne kawai na siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatai Ahmed, za su fuskanci sabbin tuhume-tuhume guda 20 a ranar 4 ga watan Yuni, 2026.
Tuhume-tuhumen sun shafi kisan kai, haɗin baki wajen aikata laifi, da sauran laifuffuka da gwamnatin jihar Kwara ta shigar a kansu game da mummunan fashin bankin Offa na shekarar 2018.

Source: Facebook
Yaushe za a fara shari'ar?
Jaridar Leadership ta ce takardar tuhumar, mai kwanan wata 9 ga Afrilu, 2026, babban lauyan jihar Kwara, Ibrahim Sulyman (SAN) ne ya shigar da ita, kuma za a miƙa wa waɗanda ake ƙarar sammaci a wannan Juma’ar, 17 ga Afrilu, 2026.
Wannan shari’a da aka daɗe ana jiranta mai lamba LWS/114C/26 tana zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa manyan mutanen da ake zargi, ciki har da Ayo Akinnibosun, wanda ya amsa laifinsa yayin shari’a cewa shi ne mai kisan gilla na daular siyasar Saraki.
Masu shigar da ƙara sun yi zargin cewa waɗanda ake ƙarar sun haɗa baki wajen ɗaukar nauyi da kuma samar wa wasu mutane makamai waɗanda ke da alaƙa da mummunan fashin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma tada hankalin jama'a.
Wadanne zarge-zarge ake yi?
Rahoton The Nation ya nuna cewa babban abin da gwamnatin jihar ta gina ƙararta a kai shi ne bayanan amsa laifi da rahotanni suka ce Ayo Akinnibosun ya yi, ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukunci a fashin.
Ana zargin ya bayyana kansa a matsayin “mai kisan gilla” da ke aiki a ƙarƙashin tsarin siyasa da ke da alaƙa da mutanen da ake ƙara.
Ana kuma zarginsa da iƙirarin cewa ya karɓi bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu daga hannun Yusuf Abdulwahab gabanin wani babban taron siyasa, tare da motar alfarma ta Toyota Lexus mai lamba ta Saraki da kuma kuɗaɗe da aka kira na “tallafin dogaro da kai.”
Ana zargin akwai hannun Saraki
A cewar masu shigar da ƙara, rukunin mutanen da ke ɗauke da makaman ana zargin sun sa hannu a wasu ayyuka da ke da alaƙa da siyasar Saraki da Ahmed.
Tuhumar ta ƙara yin nuni da iƙirarin cewa wasu daga cikin waɗanda aka yanke wa hukunci sun yi wa Saraki rakiya yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai Offa jim kaɗan bayan faruwar lamarin.
An kuma gano wasu motoci da sauran shaidu waɗanda aka ce an bi sawunsu zuwa gine-ginen gwamnati a jihar Kwara a wancan lokacin.
A baya dai kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa manyan masu laifin da suka shiga fashin.

Source: Twitter
Saraki ya sha musanta zargin
Saraki ya sha musanta duk wata alaƙa da harin, inda ya bayyana zarge-zargen a matsayin makircin siyasa da kuma yunkurin bata masa siyasa.
Tsohon Gwamna Abdulfatai Ahmed shi ma ya musanta aikata wani laifi, inda yake jaddada cewa iƙirarin da ake yi a kansa ba su da tushe.
Sanata Saraki ya yi zargi kan Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi zarge-zarge kan Muhammadu Buhari.
Bukola Saraki ya zargi marigayi tsohon shugaban kasar da gallaza masa kan sukar yawan basussukan da yake karbowa.
Saraki ya bayyana cewa majalisar dattawa da ya shugabanta daga 2015 zuwa 2019 ta sha matsin lamba daga gwamnatin Buhari.
Asali: Legit.ng


