Annoba mai alaka da kudaje ta barke a Bauchi, mutane sun fara mutuwa
- Gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar kwalara bayan gwaje-gwajen dakin bincike sun tabbatar da kamuwa da cutar a jihar
- An samu mutane 398 da ake zargin sun kamu da kwalara, yayin da mutane 16 suka mutu a kananan hukumomi 13 na jihar
- Toro ce kan gaba da mutane 231 da ake zargin sun kamu, sai Alkaleri da Kirfi da mutane 46 kowacce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi ta ayyana bullar cutar kwalara a hukumance bayan an tabbatar da wasu masu dauke da cutar ta hanyar gwaje-gwajen dakin bincike.
Gwamnatin ta ce adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar na karuwa a kananan hukumomi 13 na jihar.

Source: Original
Kwamishinan Lafiya da Jin Dadin Jama'a, Dakta Sani Mohammed Dambam, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da ranar 1 ga Agusta, 2026, wadda aka aika wa abokan huldar ci gaba da hukumomin bayar da tallafi, cewar rahoton The Nation.
A cewar sanarwar, an dauki matakin ne bayan shawarar da tawagar kula da annoba ta jihar da Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama'a suka bayar, sakamakon karuwar rahotannin gudawa mai tsanani da kuma tabbatar da kamuwa da cutar kwalara.
Gwamnatin ta ce zuwa ranar 31 ga Yuli, 2026, an samu mutane 398 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a Bauchi, yayin da mutane 16 suka mutu, abin da ya yi daidai da adadin mace-mace na 4%. An samu rahoton kamuwa da cutar a kananan hukumomi 13.
Toro ce kan gaba
Karamar Hukumar Toro ce ke da mafi yawan adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar, inda aka samu mutane 231.
Alkaleri da Kirfi sun biyo baya da mutane 46 kowacce, yayin da Ganjuwa ta samu 21. Kananan hukumomin Bauchi da Tafawa Balewa kuma kowacce na da mutane 14 da ake zargin sun kamu.
An tabbatar da yaduwar cutar
Dambam ya ce binciken dakin gwaje-gwaje ya tabbatar da cewa cutar kwalara na yaduwa a jihar, tashar Channels tv ta kawo labarin.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kaddamar da hadin gwiwar matakan gaggawa da suka kunshi sa ido kan cutar, ayyukan dakunan gwaje-gwaje, kula da marasa lafiya, ruwa, tsaftar muhalli da tsaftar jiki (WASH), rigakafin kamuwa da cututtuka da dakile yaduwarsu, samar da kayan aiki, wayar da kan jama'a kan hadarin cutar da kuma hada kai da al'umma.
“An tura tawagogin gaggawa zuwa kananan hukumomin da abin ya shafa, yayin da aka kara karfafa cibiyoyin kula da marasa lafiya tare da tattara muhimman kayan aikin kiwon lafiya domin taimakawa wajen dakile bullar cutar yadda ya kamata,” in ji shi.
Kwamishinan ya yi kira ga abokan hulda, hukumomin bayar da tallafi da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wa gwamnatin jihar da kayan aiki da kwarewar fasaha domin dakile bullar cutar da kuma hana ci gaba da yaduwarta.

Source: UGC
Annoba ta afkawa 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata annobar cuta ta afkawa sansanonin ‘yan bindiga da ke ɓoye a dazukan jihohin Nijar da Zamfara.
Barkewar cutar ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci a sansanonin hatsabiban 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng

