Nafiu Bala Ya Yi Zarge Zarge kan Kwankwaso, Ya Fadi Yadda Ya Ci Amanar Arewa
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta samu kanta cikin rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a halin yanzu
- Shugaban tsagin ADC na kasa, Nafiu Bala Gombe, ya yi zarge-zarge kan Sanaga Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya shigar jam'iyyar
- Nafiu Bala ya nuna cewa Kwankwaso ya taka rawar gani wajen hana dan Arewa yin nasara a zaben shugaban kasa na 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban tsagin jam'iyyar ADC, Nafiu Bala Gombe, soki tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Nafiu Bala ya zargi madugun na Kwankwasiyya da cin amanar Arewa gabanin zaɓuɓɓukan shekarar 2023.

Source: Twitter
Nafiu Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Premier Radio wadda aka sanya a shafin Facebook a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.
Kwankwaso ya gayyaci Nafiu kan rikicin ADC
Kwankwaso ya bar NNPP ya koma ADC ne a ranar 30 ga watan Maris, 2026, bayan watanni ana tattaunawa da shugabannin gamayyar jam’iyyun adawa.
Tun watan Yulin 2025, lokacin da gamayyar adawa ta karɓi ragamar jagorancin ADC, jam’iyyar take fama da rikicin cikin gida, inda Nafiu Bala da kuma ɓangaren da David Mark ke jagoranta kowannensu yake iƙirarin shi ne shugaban jam’iyyar.
A wata hira da DCL Hausa, Kwankwaso ya ce ya gayyaci Nafiu Bala su haɗu domin ƙoƙarin sasanta takaddamar cikin ruwan sanyi, amma shugaban ya ki amsa gayyatar.
Meyasa Nafiu ya ki amsar gayyatar Kwankwaso?
Sai dai, a hirar da aka yi da Nafiu Bala ya yi watsi da wannan iƙirari, inda ya ce ya ƙi amsa kiran Kwankwaso sannan ya soki rawar da yake takawa a siyasar Arewa.
“Kwankwaso ya kira ni yana ce mani wannan shi ne mafitar Arewa, shi ne mafita, na ce masu a'a. Na ce masu duk ranar da za a iya maganar Arewa, indai da ku ne to maganar banza ce."
"Irin wankwaso, irinsu-irinsu ba su da baki yau da za su kira ni su yi magana kan Arewa, saboda kowa ya san muradinsu suke karewa. Duk ranar da muradinsu ba su biya ba, za su zo su yi mana karya kan Arewa."
- Nafiu Bala
Wane zargi ya yi kan Kwankwaso?
Nafiu Bala ya ce a lokacin zaɓen da ya gabata, shi da sauran masu ruwa da tsaki sun roƙi Kwankwaso da ya janye wa Atiku domin gujewa rarraba ƙuri’un Arewa da kuma ƙarfafa damar yankin, amma tsohon gwamnan na Kano ya ƙi amincewa da shawarar.

Source: Facebook
"Nan zaben da ya wuce, al'ummar Arewa muka taru muka ce ya yi hakuri ya duba girman Allah ya kyale tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, don ya fito daga yankinmu, ka da ya goyawa wata jam'iyya baya."
"Amma abin mamaki sai muka ga ya je ya dauko wata karamar jam'iyya wadda iya Kano ya tabbatar ba cin zabe zai yi ba, ya yi amfani da ita domin ya rage kuri'un Arewa, har ya ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dama ya ci zabe."
"To wannan abin ba mu manta shi ba kuma al'ummar Najeriya ba su manta ba, al'ummar Arewa ba za mu manta da wannan abin ba."
- Nafiu Bala
Kwankwaso ya aika sako ga INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwarsa kan hukumar INEC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya nuna bangaranci karara da hukuma zabe take yi.
Kwankwaso ya ce ya hada kai da sauran shugabannin hadakar siyasa da kuma masu kishin dimokuradiyya domin yin Allah-wadai da yadda hukumar zabe ta sako ADC a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


