Iran Ta Kasa Binne Ayatollah Khamenei Fiye da Kwanaki 40 bayan Rasuwarsa, an Ji Dalili

Iran Ta Kasa Binne Ayatollah Khamenei Fiye da Kwanaki 40 bayan Rasuwarsa, an Ji Dalili

  • Gwamnatin kasar Iran ba ta gudanar da jana'izar tsohon jagoran addini, Ayatollah Ali Khemanei, kwanaki da dama bayan rasuwarsa
  • Ayatollah Ali Khamenei dai ya rasa ransa ne sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
  • Wani masani ya haska dalilan da yake ganin sun sanya gwamnatin Iran ba ta binne Ayatollah Khamenei ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

​Birnin Tehran, Iran - Har yanzu ba a nuna wurin da za a binne tsohon Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ba.

Jami’an Iran na nazarin matsalolin tsaro game da yadda taron jama’a zai kasance a irin wannan jana'iza mai girma, yayin da wani masanin tsaro ke iƙirarin cewa jinkirin ya faru ne saboda fargabar da ke tattare da birnin Tehran.

Ali Khamenei ya rasa ransa a hare-haren Amurka da Isra'ila
Tsohon jagoran addini na kasar Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Tashar New York Post ta kawo rahoto kan dalilin da ya sanya ba a binne marigayi Ali Khamenei ba.

Kara karanta wannan

Lebanon ta watsa wa Trump kasa a ido, ta dauki mataki na ban mamaki kan Isra'ila

Amurka da Israila sun kashe Ali Khamenei

Ali Khamenei, ɗan shekara 86, an kashe shi ne a wani harin sama na haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026. Har yanzu ba a binne gawar malamin ba, lamarin da ya saɓawa tsohuwar al'ada.

Jana'izar gwamnati ta kwanaki da dama da aka yi wa wanda ya gabace shi, Ayatollah Ruhollah Khomeini, a shekarar 1989, ta sanya miliyoyin mutanen Iran sun cika titunan Tehran suna makoki.

Amma irin wannan yanayin na Khamenei bai samu ba yayin makonni na hare-haren sama masu tsanani a faɗin Iran waɗanda suka halaka da dama daga cikin manyan shugabannin gwamnatin kasar.

Meyasa Iran ba ta binne Khamenei ba?

Tehran ba ta da ikon gudanar da irin wannan gagarumin taron tunawa da shi yayin da yaƙin yake cikin yanayi na tsagaita wuta mai cike da dar-dar, in ji Behnam Taleblu daga gidauniyar Foundation for Defense of Democracies.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

“A taƙaice dai, gwamnatin tana tsoro sosai kuma tana da rauni wajen gudanar da jana'izar."

- Behnam Taleblu

Dalilan da suka sa ake guje wa gudanar da bikin sun haɗa da haɗarin yiwuwar kai hare-haren sama daga Isra'ila, zanga-zangar nuna adawa irin wadda aka yi a faɗin ƙasar a farkon wannan shekarar.

Hakazalika, akwai buƙatar gwamnatin ta bayyana dalilin rashin ganin Mojtaba Khamenei, ɗan Khamenei kuma sabon jagoran addini na kasar wanda ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan naɗa shi.

Khamenei ya rasa ransa a hare-haren Amurka da Isra'ila
Marigayi Ayatollah Ali Khamenei, tsohon jagoran addini na Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Masani ya yi magana

“Hakan yana nuna cewa taron jana'izar Ruhollah Khomeini da ya kafa gwamnati a shekarar 1989 ya kasance babban al'amari, amma wanda ya gaje shi har yanzu ba a iya yi masa jana'iza ba bayan fiye da wata guda da mutuwarsa."
“Jamhuriyar Musulunci tana son yin kurari game da iko da tituna, amma katse intanet na tsawon kwanaki 50 ya gaya maka duk abin da kake buƙatar sani. Gwamnatin tana tsoron sakamakon fitar gaskiya fili.”

- Behnam Taleblu

Kara karanta wannan

Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu

Jaridar The Australian ta rahoto cewa a yanzu jami'an Iran suna nazarin birnin Mashhad da ke can Arewa maso Gabashin ƙasar a matsayin wurin da za a iya binne shi.

Iran ta gindaya sharadi ga Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta gindaya sharadin sake tattaunawa zagaye na biyu da Amurka.

Gwamnatin Iran ta ce za ta iya amincewa a ci gaba da tattaunawa bisa sharadin cimma matsaya kan tsarin da za a bi.

Ta jaddada cewa matukar ba a tsaida tsari da ka'idojin da za a bi a zaman sulhun ba, ba za ta amince ta koma wurin tattaunawa a karo na biyu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com