Tofa: Kamala Harris Ta Fallasa Dalilin Trump na Fara Yaki da Iran
- Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta taso Shugaba Donald Trump a gaba kan yakin da ya fara da Iran
- Kamala Harris ta bayyana cewa akwai abin da Donald Trump yake son karkatar da hankalin jama'a kansa, shiyasa ya fara yaki da Iran
- Tsohuwar 'yar takarar shugaban kasar ta bayyana cewa Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu ne ya ja hankalin Trump kan yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Michigan, Amurka - Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta yi magana kan yakin Amurka da Israila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamala Harris ta ce shugaban Amurka, Donald Tump na amfani da yaƙin Iran ne domin karkatar da hankalin jama’a.

Source: Getty Images
Tashar BBC Hausa ta kawo rahoton cewa Kamala Harris ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wani taron mata na jam'iyyar Democrat a jihar Michigan.

Kara karanta wannan
Iran ta kasa binne Ayatollah Khamenei kwanaki fiye da 40 bayan rasuwarsa, an ji dalili
Amurka da Isra'ila sun kaddamar da yaki kan Iran
Kasashen Amurka da Isra'ila dai sun kaddamar da hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.
Hare-haren dai sun yi sanadiyyar hallaka jagoran addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan kwamandoji da jami'an gwamnatin kasar Iran.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Israila da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Wane dalili Kamala Harris ta ba da?
Tsohuwar yar takarar shugaban kasar ta Amurka ta bayyana cewa Donald Trump na amfani da yakin ne domin kawar da hankalin jama'a daga sakin bayanan badakalar Jeffrey Epstein.
Kamala Harris ta nuna cewa an yi wa Shugaba Trump shigo-shiga ba zurfi ne kan fara yaki da kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ta nuna cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ne ya ingiza Shugaba Trump wajen fara yaki da Iran.
Sai dai, tsohuwar 'yar takarar shugaban kasar ta jam'iyyar Democrat ba ta bayar da hujja ba kan iƙirarin nata.

Source: Facebook
Kamala Harris ta ce an ja Trump fara yaki da Iran
Amma duk da hakan, ta bayyana cewa Amurkawa ba sa son yaƙin da ake yi a Iran, tashar Fox News ta kawo rahoton.
“Ya shiga yaƙi wanda Bibi Netanyahu ne ya jawo shi cikinsa, bari mu fito fili mu faɗi hakan, ya shiga yaƙin da al’ummar Amurka ba sa bukata, wanda kuma ya jefa rayuwar dakarun Amurka cikin haɗari.”
- Kamala Harris
Har ya zuwa yanzu dai ba a samu wani martani daga Shugaba Trump kai-tsaye kan zarge-zargen na Kamala Harris ba.
Amurka ta gabatar da sabon tayi ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Iran ta bayyana cewa tana nazarin sababbin sharuddan da Amurka ta gabatar mata.
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa ba za ta yi sassauci ba kan manyan muradunta duk da cewa Amurka ta sauya sharuddanta.
Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Saeed Khatibzadeh, ya jaddada cewa dole ne kowace yarjejeniya ta kare haƙƙin Iran ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Asali: Legit.ng
