Za a Samu Alheri: Manhajar X Ta Canza Salo, Ta Kawo Sabon Tsarin da Mutane Za Su Samu Kuɗi
- Dandalin sada zumunta na X wanda a baya aka fi sani da Twitter zai dakatar da shirin raba kudaden shiga a ranar 7 ga Satumba, 2026
- X ya kuma bayyana sabon tsarin da ya kawo, wanda zai bai wa masu amfani da shafin, musamman masu wallafa abubuwa, damar samun kudi
- Kamfanin ya ce za a fara karɓar buƙatun shiga sabon tsarin samun kudi a X daga ranar 8 ga Satumba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United State - Dandalin sada zumunta na X, wanda a da aka fi sani da Twitter, ya sanar da cewa zai dakatar da shirin rabon kudaden shiga ga masu ƙirƙira bidiyoyi, hotuna da sauransu.
Kamfanin da ya mallaki X ya kuma ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna Original Content Rewards Program, wanda zai ba mutane damar samun kudaden shiga ta hanyar wallafa abubuwan kirkira.

Source: Getty Images
The Cable ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, kamfanin ya ce sabon shirin zai bai wa masu ƙirƙirar bidiyoyi, hotuna na asali damar samun lada saboda samar da abubuwan da ke taimakawa wajen bunkasa tattaunawa a dandalin.
Kamfanin ya ce tsohon shirin zai ƙare a ranar 7 ga Satumba, 2026, amma masu ƙirƙira da ke cikin shirin a halin yanzu za su ci gaba da samun kudaden shiga har zuwa wannan rana.
“A yau, muna ƙaddamar da sabon tssri, wata sabuwar hanya da masu amfani da X za su samu kudade ta hanyar wallafa abubuwan asali da kuma bayar da gudunmawa mai ma'ana ga tattaunawa,” in ji kamfanin.
Kamfanin zai biya kudaden ƙarshe
X ya ce wadanda ke cikin tsohon shirin rabon kudaden shiga za su ci gaba da samun kudaden su har zuwa ranar 7 ga Satumba, 2026.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa za a biya kudin ƙarshe na tsohon tsari a ranar 11 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027
“Idan a halin yanzu kana cikin tsohon tsarinmu, za ka ci gaba da samun kudade har zuwa 7 ga Satumba, 2026, sannan za a fitar da kudin rabonka na ƙarshe a ranar 11 ga Satumba, 2026,” in ji sanarwar.

Source: Getty Images
Yaushe sabon shirin zai fara?
Kamfanin ya ce za a fara karɓar buƙatun shiga sabon tsarin samun kudi a X daga ranar 8 ga Satumba, 2026, amma sai masu neman shiga sun cika sharuddan cancantar shirin.
Masu ƙirƙirar bidiyoyi, hotuna da wallafa labari na asali za su iya duba ko sun cancanta ta Creator Studio, a sashen Original Content Rewards.
Rasha za ta yi shari'a da mai Telegram
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Rasha ta zargi Telegram da kin dakatar da tashoshin da ake amfani da su wajen daukar ma'aikata domin ayyukan ta'addanci
Hukumar tsaron cikin gidan kasar ta fitar da sammacin kama Pavel Durov, mamallakin Telegram, tana zarginsa da taimaka wa ayyukan ta'addanci.
A baya, Durov ya taba zargin gwamnatin Rasha da kirkirar sabbin dalilai domin takaita wa 'yan kasar damar amfani da Telegram.
Asali: Legit.ng
